Home / Labarai / AIKIN HAJJI : AN GANO MATA 75 MASU CIKI A MAKKA DA MADINA

AIKIN HAJJI : AN GANO MATA 75 MASU CIKI A MAKKA DA MADINA

DAGA IMRANA ABDULLAHI

Dokta Usman Galadima ya tabbatar da cewa a can kasa mai tsarki da yan Najeriya ke gudanar da aikin Hajji a halin yanzu an gano mata masu dauke da Juna biyu har guda 75 da cikin nasu yake cikin hali daban daban.

A Makka akwai 45 sai kuma a garin Madina akwai mata 30 duk dauke da Juna biyu.

Abin jira a gani dai a halin yanzu ko kasar Saudi Arabiya za ta yi magana a game da lamarin ko yaya? Ganin cewa a can kwanan baya an yi wani lokacin idan za a ta fi aikin Hajji ba a barin mata masu dauke da Juna biyu su je aikin Hajji alhali suna dauke da ciki.

Aikin Hajji dai na cikin tukunnan musilinci da idan mutum nada iko wato halin zuwa zai je a kalla sau daya a rayuwarsa.

Amma a irin yadda wadansu mutane suka mayar da lamarin mai yuwuwa ko domin wadatar da Allah ya ba su ko kuma domin wata manufar da su kadai suka san da ita sai su rika zuwa aikin Hajji a duk lokacin da suke da bukata.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.