Daga Imrana Abdullahi
Sabon mashawarci na musamman ga gwamnan iharJ Kebbi kan harkokin Gwamnati da samar da ababen more rayuwa, Alhaji Abubakar Malam (Shettiman Gwandu) ya yi kira da kowa ya bayar da hadin kai domin ci gaban Jihar Kebbi.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da Sa hannu Ahmad Idris, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kebbi da aka rabawa manema labarai.
Mai ba da shawara na musamman a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Birnin Kebbi ya ce, “Jahar Kebbi a halin yanzu tana bukatar goyon bayanmu na hadin gwiwa don yin fice a kowane fanni, dole ne mu hada kai, mu fito da abubuwan da suka shafi al’umma da masu zaman kansu, mu hada kai da sabbin abubuwa.
shugabanci da kuma yin aiki tare da burin iyayenmu da suka assasa su na ganin jiharmu mai kauna da dora ta a kan matsayinta a fagen ci gaban siyasa da tattalin arzikin kasa”.