Home / Labarai / An Karawa Litar Mai Farashi A Najeriya

An Karawa Litar Mai Farashi A Najeriya

 

….A Abuja 617 A Legas 568
Daga Imrana Abdullahi
Shugaban kamfanin kula da hada hadar Mai fetur Mele Kyari ya tabbatar da karin farashin man

Da yanzu za a rika shan man fetur a duk lita daya kamar yadda ya bayyana a garin Abuja naira 617 yayin da a Legas kuma za a rika sayar da litar a kan naira 568.
Tun lokacin da wannan Gwamnatin APC karkashin shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ta Dare ragamar mulkin kasar farashin man fetur ya zamarwa yan Najeriya wata babbar matsalar da a halin yanzu kowa yaro da babba ke kokawa a kan batun yadda dukkan kayan masarufi da na yau da kullum baki daya suka yi tashin Gwauron zabi da a wasu wuraren ma lamarin ya gagari kundila.
A game da batun harkokin sufuri mutane da yawa tun da farashin ya kai naira 540 ababen hawan suka gagari masu shi sai ajiyewa.
Da wannan karin farashin na yau kuma wakilin mu yaji wadansu jama’ar da dama na cewa kodai su sayar da ababen hawan ko kuma idan za su yi haya ne domin ciyar da iyali su karawa jama’a farashin su ko nawa farashin zai kama.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.