Home / Labarai / BA MU DA SHAKKA  A KAN KOTU NAN MA’AIKATAR SHARI’A TA JIHAR KADUNA – LAUYA MARCUS BOBAI

BA MU DA SHAKKA  A KAN KOTU NAN MA’AIKATAR SHARI’A TA JIHAR KADUNA – LAUYA MARCUS BOBAI

 

 

Lauyan Gwamnati a Jihar Kaduna Joseph Marcus Bobai, ya bayyana cewa ba tare da wata shakka ko ga ma’aikatar shari’a ko Kotun da ke sauraren karar da suka shigar ta kisan kai da ake yi a halin yanzu

A matsayina na lauyan Gwamnatin Jihar Kaduna kuma a tare da shi akwai abokin aikinsa da suke aikin tare da shi wato Ibrahim Shu’aibu dukkansu daga ma’aikatar shari’a ta Jihar Kaduna.

 

Ya ce a yau Litinin 17 ga watan Yuli, 2023 babbar kotu ta 9 ta ci gaba da zaman shari’a inda aka saurari mai bayar da sheda na shida da suka gabatar a gabanta da ake kira PW 6 da wannan ne duk mun kammala gabatar da shaidun mu a gaban kotu.

 

Don haka “Za mu koma a gaban kotu a ranar 2 ga watan 8 wato Agusta mai zuwa domin jin ta bakin wanda ake tuhuma da wannan laifin kisan kai domin aji kariyar da zai yi a matsayin martani na kariyar kai ga tuhumar da ake yi masa”, inji Joseph Marcus Bobai.

 

Lauyan wanda ke yi wa Muhammad Giwa da ake wa zargi da yin kisan kai ya shaidawa manema labarai cewa

Lauya Chief chris Ekhasemomhe, mai tsayawa wanda ake zargi da laifin kisan kai Muhammed Muhammad Giwa, da ake zargi da aikata laifi na farko.

 

Lauyan ya ce abin da ya faru a yau a kotun shi ne Dan Asabe ya gabatar da bayanan sa a kan abin da ya Sani a wannan shari’a da ake yi a gaban kotu kuma ni kaina na yi masa tambayoyi a game da abin da ya fadi.

 

Kuma amfanin yin wannan tambayoyi da Lauyoyi ke yi shi ne domin tabbatar da gaskiyar wanda ya bayar da shaida a game da wani laifin da ake shari’a a kansa domin ganin ko ya na fadin gaskiya amma dai kotu ce keda ikon tabbatar da laifi a kan kewaye.

 

” A game da ko ina murna da farin ciki ko A’a ba haka abin yake ba, domin kotu ce keda iko a kan kowace shari’a ba Lauya ba. Shi dai Lauya na yin aikinsa ne kawai haka nan nima aiki na nake yi, sai dai kawai ina murna domin a yau sun kammala gabatar da shaidu a gaban kotu”.
Sai dai kawai mun cimma matsaya a kan ranar da za a gabatar da bayanan wanda ake kara da ake zargi da aikata laifi.

 

A game da hakan ne muka cimma matsayar ranar 2 ga watan Agusta 2023 domin mu gabatar da kariyar zargin da ake yi mana.
Sai dai ” Ni ban taba neman kotu ta bayar da belin wanda nake tsayawa ba domin idan kana aikin Lauya zaka rika duba lafiyar wanda kake yi wa da farko.

 

 

Idan kai Lauya ne kana yin aiki kamar irin wannan zaka rika Sanya batun kariyar wanda kake yi wa kariyar a matsayin Lauya domin kada a samu wata matsala ga wanda ake zargi kuma daga baya sai kotu ta gano bashi da laifi domin tun farko zarginsa ne kawai ake yi, kaga an kashe mutum a banza haka kawai saboda haka ne ban ta ba neman a bayar da shi beli ba domin ina yin aikin Lauya irin wannan da dadewa”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.