…Muna kuma taimakawa matasa su dogara da kansu ta hanyar sana’a
Daga Imrana Abdullahi
Honarabul Auwal Yahaya Yahaya ake yi wa lakabi da yaro mai kyau, da ke wakiltar mazabar Unguwar Sanusi cikin karamar hukumar Kaduna ta Kudu ya bayyana cewa a kullum yana Son ya bar abin da za a rika tunawa da abin da na yi na alkairi da yake amfanar jama’a masu yawa hakika a nan hankali na ya fi karkata”
Ya kara da cewa duk da cewa aikin dan majalisa shi ne aikin yin doka ko gyaran doka, amma duk da hakan akwai wadansu abubuwa da dama wanda ko dai alfarma ko kuma kudanci da Gwamnati hakan ta Sanya zaka ga ayyuka da yawa an yi su a cikin mazaba ta ko dai daga Gwamnatin tarayya ko kuma daga Gwamnatin Jiha Wanda sanadiyya bibiya da kuma neman yadda za a yi aka same su.
Ban da kuma aikin taimakawa jama’a da ya kasance wani lamari ne ga mutumin da yake da shi ba wai dan siyasa kawai ba, saboda haka wannan wata gaba ce da ta zamar mana wajibi.
“Saboda haka ina son kowa ya Sani duk wanda aka zabe shi lallai wahala ce, dagewa da jidali na al’umma domin haka ne idan ka yi nesa da al’umma ka bar siyasa tabbas idan baka da al’umma a siyasa ba zaka yi tasiri ba, amma ko baka da ko Kwabo idan al’umma na son ka hakika ka fi dan Gote”.
Hakan ta Sanya ni a kullum abin da nake kallo shi ne ta inda aka samu matsala musamman idan muka dubi abin da ya shafi maganar karatu a Jihar Kaduna muna godiya ga mai girma Gwamnan da ya gabata Malam Nasiru Ahmad El – Rufa’i wanda kafin zuwansa ana bayar da ilimi kyauta ne daga Firamare zuwa karamar Sakandare ne amma sai da ya mayar da shi daga Firamare da Sakandare duk kyauta ne wannan na nufin cewa ba wanda zai ce ba a bashi damar ya yi karatu ba, sai dai meye ya zama tarnaki yake samun dan talaka da aka gina makarantun Gwannati domin su saboda mafi yawan yayan masu kudi da yaya irin na mu makarantun kudi suke zuwa”,
Amma kuma mutanen da suka fi yawa a cikin al’umma da suke da kashi Tamanin ko Tamanin da biyar wadanda kuma suke yin zabe, amma kuma an fishi cin ribar zaben makarantun Gwannati suke zuwa kuma idan mutum ya samu tsallakewa daga makarantar karamar Sakandare zuwa kammala Sakandare aji shida to, komai sai ya tsaya kawai saboda babu yadda za su iya biyan kudin jarabawar fita Sakandare ta WAEC ko NECO hakan yasa muka kalli irin wadannan abubuwan”.
“Hakika mun kalli irin hakan halin da jama’a suke ciki akwai mutane kusan dari da Hamsin a lokacin biyan kudin jarabawar fita Sakandare ta WAEC mukan dauki mutane kamar dari mu biya masu da kudin ba domin ba mai ba mu ko Kwabo kawai dai mutum ya rubuta jarabawar kawai ya ta fi kyauta, saboda mun fahimci cewa batun biyan kudin jarabawar fita Sakandare na kawo matsala har da yawan matasa ke tsayawa ba su iya ci gaba da karatun. Kuma kafin inzo Gwamnatin nan duk ina yi amma da na zo sai na kara karfafa abin saboda na fahimci cewa daukar kudi ka ba matashi ba shi ne mafita ba idan mutum ya zamanto ya na da ilimi shi zai nemawa kansa abin da zai yi”.
Dan majalisa Auwalu Yahaya ya kara da bayanin cewa ya kuma fahimci cewa wasu matasan kuma koda sun yi jarabawar fita Sakandaren wasu maganar naira dubu biyar na jarabawar JAMB wani aiki ne a nan ma ya ce “ya na kallon abin kuma ya na shiga ciki dai dai Gwargwado sannan dadin dadawa abin da ya shafi matasa musamman mata in ka same su a cikin kashi dari kashi Sittin zuwa Sittin da biyar na matasan matan mu suna sha’awar yin karatun asibiti domin kula da kiwon lafiya musamman makarantun jinya da unguwar Zoma kasancewa abu ne da zai taimakawa addini ta yadda mace za ta duba mace kuma Namiji ya taimakawa Namiji dalilin da yasa kenan muka dage wajen biya masu kudin tallafi na karatu “scholarship” domin suke su koyo karatun.
Kuma a wannan karon ma a mazaba ta duk mazaba mun dauki mutane Goma wssu ma har Arba’in wanda daman an yaye wasu kuma zamu kara daukar wasu kuma suna kammala za mu kara daukar wasu duk bayan wata uku ko shida, sannan a cikinsu akwai wadanda idan an san suna da kokari kwazo da himma sai a tura su duk su yi gaba wato makarantu na gaba kenan saboda haka ne a cikin wadanda muka fara yi na farko sai muka fahimci akwai guda biyu masu kwazo kwarai duk mun ba su dama su ci gaba domin a haka ne zaka taimaki jama’a kasancewa ba abin da zaka yi da ya wuce aba mutum ilimi ya kuma samu sana’ar da zai yi.
Ba za a iya ba matasa kudi ba a hannu domin wani matashin sai kaga a hannunsa akwai wata mai tsada amma ba sana’a, to amma muna ganin gina su da sama masu sana’a abu ne mai kyau kuma duk mai sana’a za mu ci jin karfin taimakon mutum ya taimaki kansa a kan sana’ar da yake yi.
Honarabul Auwalu Yahaya ya kuma ja hankalin matasa da su mayar da hankalin wajen rungumi Sana’oi ta yadda kowa zai tsira da mutincinsa da kuma dogaro da kai.
Hakika rungumar sana’oi ne zai kare masu mutuncin kan su da na iyalinsu, musamman awannan lokacin da muke ciki.
Honarabul Yahya Auwalu Muhammad( Yaro Maikyau) Dan majalisan Jihar Kaduna Mai wakiltar mazabar unguwan Sanusi shine yayi wannan gargadi gami da Jan hankalin jiya a Kaduna Jim kadan bayan ya karbi lambar yabo da karramawa daga Kungiyar Mawallafa da Marubuta Mujalla ta bangaren Arewacin Najeriya.
Yayin da yake mika masa lambar yabon shugaban Kungiyar Dokta Sani Garba ya bayyana ce wa Dan Majilisar ya cancanci wannan karramawarne saboda jajircewassa wajen tallafawa talakawa da marassa galifu musamman a fannin ilimi, koyar da sana’a don dogaro da Kai da Kuma tallafawa tsofaffi da zaurawa da sauran ayyukan Jin kan al’umma, wannan yasa Kungiyar ta zakulo shi don ta yaba masa Kuma ta karfafamasa gwaiwa don ci gaba da irin wannan bada gudumowa ga al’umma.
Yayin da yake Mai da Jawabi Hon. Auwal Yaro Maikyau ya godewa Allah madauki sannan Kuma ya godewa wannan kungiya da ta duba irin ayyukan da yake yi Kuma ta ga ya dace karrama shi, ya Kuma kara da Jan hankalin matasa da su nemi sana’a don gwabnati bazata iya bawa kowa aiki ba, amma in kana da sanarda kake yi to Mai kudin ko Dan siyasa zai fi Jin dadin temakawa Mai sana’a
Dan Majalisan Kuma ya yabawa Gwabna Uba Sani ganin irin canjin da ya kawo a Jihar Kaduna a cikin kwana dari musamman rage kudin manyan makarantun da ya yi abin a yaba masa ne kwarai.