Home / Labarai / Gwamnatin Kano ta kori Jami‘an ta biyu

Gwamnatin Kano ta kori Jami‘an ta biyu

 

Daga Imrana Abdullahi

A wani matakin da Gwamnatin Jihar Kano ta dauka domin zama matakin gargadi ga masu sakin baki suna yin kalaman da suka ga dama yasa Gwamnatin jihar Kano ta sallami Kwamishinan Kasa  na jihar Adamu Aliyu Kibiya da kuma mai bai wa Gwamna Shawara Kan Harkokin Matasa Yusuf Imam da aka fi sani da Ogan Boye.

Kwamishinan yada labarai na Jihar Baba Halilu Dantiye ne ya jagoranci taron manema labarai inda ya bayyana wannan mataki.

Kwamishinan ya kuma gargadi dukkan masu rike da mukaman gwamnati da su iya bakin su daga kalamai marasa kan gado.

An sauke jami‘an ne bisa wasu kalamai na yin barazana ga alkalan da suke sharia‘ar kararrakin zaben Gwamnan jihar.

About andiya

Check Also

NA 8 Div Sokoto new GOC,  General Ibikunle assumes

S. Adamu, Sokoto A new GOC for the 8 Division Nigerian Army, Sokoto , appointed …

Leave a Reply

Your email address will not be published.