Daga Bashir Bello Majalisa, Abuja.
Dan Majalisar Taraiya mai Wakiltar Mazabar Borno ta Tsakiya , Sanata Kaka Shehu Lawan ya ga batar da wani Kuduri na gaggawa a gaban zauren Majalisar Dattawa da ke Abuja.
Majalisar Dattawa ta umarci Kwamitocinta na Sharia da na Yancin Dan’adam da na Dokoki ba tare da bata lokaci ba su fara shiri domin tattara Dokoki da aka yi a Kasar nan daga shekara ta 2004 zuwa shekara ta 2023 a tarasu guri daya.
Sanatan ya ce dalilin sa na gabatar da wannan Kuduri shi ne ya lura cewa kimanin shekaru 19 kenan da aka tattara Dokokin Kasarnan wanda hakan ya haifar da rudani a Kasa inda ake amfani da Dokoki daban-daban ma su karo da juna.
Kaka ya kara da cewa ya lura cewa masu tallar littattafai akan titunan Kasarnan su na dauke da Kundin na Shari’a irin daban-daban wanda hakan koma baya ne a kasa.
Ya kara da cewa, ya lura Malaman Makarantu a Jami’a da Dalibai kai harma da Lauyoyi suma suna amfani da Kundin Dokokin na Kasar iri dabab-daban wanda hakan bai da ce ba.
Sanatan ya ci gaba da cewa, tun wancan lokaci zuwa yanzu Majalisar Tarayya ta yi Dokoki masu tarin yawa wadanda Shugabannin Kasa daban-daban sun saka masu hannu amma har ya zuwa yanzu ba a tattara wadannan Dokoki ba guri guda domin amfanar yan Najeriya ba.
Sanata wanda ya karawa mane ma labarait haske a ofishin! sa ya ce Dokace ta sahalewa ofishin Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Taraiya da ya gabatar da wannan bukata ta tattara Dokokin na Kasa tare da hadin gwiwa da Majalisar Taraiya.
Sanatan ya kara da cewa idan aka har-hada wadannan Dokoki guri guda zai taimaka wajen gudanar da shari’a a Najeriya ba tare da kawo rudani ba.
In da ya ce a halin yanzu tabbas akwai rudani a yadda ake yanke hukunce hukunce a Kotunan Najeriya sakamakon bambance – bambance da ake samu a Kundun Shari’a.
Majalisar ta Dattawa ta umarci Kwamitocin nata dasu hanzarta tuntubar Babban Lauyan Gwamnatin Taraiya don fara tattara wadannan Dokoki guri guda ba tare da bata wani lokaci ba. Tare da sanar da ita halin da ake ciki, cikin sati biyu masu zuwa.