Daga Imrana Abdullahi
Alhaji Rabe Mela Maska da ke karamar hukumar Funtuwa ya yi kira ga Gwamnan Jihar Katsina Dokta Dikko Umar Radda da ya taimaka masu da aikin hanyar da ta tashi tun daga martabar Maska zuwa Maska, Tumburkai da sauran wadansu garuruwa da dama a yankin.
Haka zalika Rabe Mela Maska ya kuma yi kira ga Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Dikko Umar Radda da ta gina masu Dam wanda a can baya har an fara kawo kayan aiki irin su duwatsu da sauransu domin gina masu Dam tun daga Gadar Maska domin amfanin al’ummar kasa baki daya.
“Muna fatan Allah ya sa Gwamna Diko Radda ya gama lafiya, Allah ya saka masa da alkairi kuma bukatunsa na alkairi Allah ya biya masa, yadda sauran Gwamnoni suka yi shekaru Takwas suka gama lafiya shima Allah ya taimake shi ya gama Mulkinsa lafiya domin hakika ya na taimakawa Talakawa kwarai matuka kuma muna jin dadi fiye da kima”, inji Rabe Mela Maska.
Sai dai Alhaji Rabe Mela Maska ya koka a kan wata hanyar da tsohon Gwamnan Jihar Katsina Barista Ibrahim Shehu Shema ya yi daga marabar Maska zuwa Maska ta hada da wadansu garuruwan da ake samar da amfanin Gona da yawa inda ya ce wannan hanya ta lalace har ta kai ga zama tarkon mutuwa baki daya.
Daga ” Tudun iya, Maska zuwa Tandu, Tumburkai zuwa Kaura, Sabon Gida da Dan tankari duk a halin yanzu wannan hanya ta lalace bata biyuwa cikin dadin rai duk da irin yadda ake fitowa da dimbin kayan amfanin Gona, saboda haka ne muke yin kira ga Gwamnan Jihar katsina da muma a taimaka mana kamar yadda ake ta bayar da hanyoyi muma a san da mu ayi mana wannan hanya da na ambaci garuruwan da ta ratsa domin a gyara mana mu san a cikin Jihar muke”.
Sai kuma na biyu “ga mu da gada, an kawo kayan aiki tun wajen shekaru Goma an yi dakin Dam amma har dakin ya lalace. Amma tun da a yanzu lokaci ne na Noman rani idan an datse Dam din a duk yankin nan ko daga ina lamarin zai ta fi dai dai ayi ta Noman rani a koda yaushe. Misali idan mutum ya yi tafiyar kilomita Ashirin gabas da Yamma kudu da Arewa duk zaka ga ba Dam ga kuma dimbin manoma ta ko’ina kuma a shirye suke su yi Noman rani amma ba Dam.
Saboda haka muna yin kira ga mai girma Gwamna da ya taimaka ya sa ayi mana wannan Dam domin a samu yin Noman rani tun da duk ga Gonaki nan ba iyaka ta ko’ina a shimfida.
” A nan Gadar Maska ne aka ajiye kayan yin Dam da suka hada da Dutse da daki a wurin amma a halin yanzu duk sun watse ba komai
Da wakilin mu ya tuntubi wadansu mutane a garin Funtuwa sun yi kira ne ga Gwamnan Jihar Katsina da ya gudanar da bincike game da wannan maganar yin Dam a gadar Maska domin gano inda aka tsaya .