Home / Labarai / Wailare Ya Mika Sakon Ta’aziyya Ga Iyalan Bukar Makoda

Wailare Ya Mika Sakon Ta’aziyya Ga Iyalan Bukar Makoda

Daga Imrana Abdullahi

Za a ci gaba da tuna babban Gwarzo dan kishin kasa da son jama’a Alhaji Bukar Makida sakamakon irin ayyukan da ya aikata wajen ci gaban kasa da al’ummarta baki daya.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sakon ta’aziyya da aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Laraba da shugaban cibiyar Tamallan, Dokta Sale Musa Wailare,ya sanyawa hannu, inda ya bayyana marigayi Alhaji Bukar Makida a matsayin wani ginshikin yin koyi a wajen samar da ci gaban kasa ba kuma a Jihar Kano kawai ba har ma da kasa baki daya.

“Hakika mun yi rashin Uba da a koda yaushe yake ba mu shawarwari a duk lokacin da muka je inda yake, kuma mun yi ko yi kwarai daga rayuwarsa musamman a game da batun hadin kan kasa, Dimokuradiyya da kuma son Juna a koda yaushe. A madadin Daraktoci, ma’aikata da dukkan ma’aikatan cibiyar Tamallan, ina mika sakon ta’aziyya ga Honarabul kwamishina na ma’aikatar Ruwa Dokta Ali Haruna Makoda da kuma dukkan al’ummar karamar hukumar Makida Bali daya a game da wannan babban rashin da aka yi”, inji shi.

Dokta Sale Musa Wailare, wanda ya kasance fitaccen dan siyasa ne da ya bayar da gudunmawa wajen ci gaban Dimokuradiyya ya ce zai ci gaba da kasancewa a kan gaba a kokarin kawo ci gaban kasa musamman ta hanyar samar da ayyukan yi a Mazabar dan majalisar  Dan batta da Makoda baki daya.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.