Home / Big News / An Shawarci Mawadata Su Yi Amfani Da Kudin Zuwa Umara Wajen Ciyar Da Mabukata
Jihar Taraba na da arzikin Katako inda ake sarrafa shi wajen yin abubuwa daban daban har da kwanukan cin abinci kamar yadda zaku gani a wannan hoton

An Shawarci Mawadata Su Yi Amfani Da Kudin Zuwa Umara Wajen Ciyar Da Mabukata

An Shawarci Mawadata Su Yi Amfani Da Kudin Zuwa Umara Wajen Ciyar Da Mabukata
Mustapha Abdullahi
Alhaji Zayyanu Aliyu, dan asalin Jihar Sakkwato ne ya yi kira ga mawadata da su yi amfani da kudin da ba su je kasar Saudiyya domin umara ba su ciyar da mabukata a wannan wata na Azumin Ramadana, domin samun lada da ci gaban kasa baki daya.
Alhaji Zayyanu, ya ci gaba da cewa batun ciyar da mabukata zai zo ne a daidai irin wannan lokacin da aka fara Azumi bana.
” kuma a bisa la’akari da irin yadda cutar Covid – 19 da ake kira da Korona ta lalata Tattalin arzikin Nijeriya da kuma na duniya baki daya, hakika taimakawa Mabukata zai kawo gagarumin ci gaba ba dukkan wanda ya taimakawa jama’a musamman mabukata kuma acikin irin wannan wata mai Albarka”.
” Ya dace a canza batun zuwa aikin umara na mutum daya, musamman tun da mahukuntan kasar Saudiyya sun haka zuwa Umara Bana sakamakon matsalar ciwon da ya addabi duniya,” Aliyu ya kara da bayanin hakan.
Kamar yadda Aliyu ya bayyana cewa idan mawadata suka taimakawa masu bukatar da ke cikin al’umma zai taimaka a samu saukin matsalar da ciwon da ya addabi duniya ta Jefa mutane a ciki a game da tattalin arziki wanda Nijeriya na ciki.
Halin da batun zaman gida ya Jefa jama’a sakamakon dokar hana fita da ake sanyawa a Nijeriya ya cancanci masu wadata su duba halin da mabukata ke ciki, saboda mutane ba su iya fita daga gidajensu balantana ayi maganar neman abinci da sauran kayan masarufi kuma ga Azumi mutane na yinsa duk da halin da duniya ta shiga.
Aliyu ya ci gaba da cewa ” Ya dace mawadata da suke zuwa aikin Umara a shekara musamman lokacin da ake ciki na Azumi su yi amfani da dukiyarsu su ciyar da jama’a ko a ba mutane kayan abinci da sauran kayan bukatun yau da kullum da mutane ke bukata”.
” Ya kamata a yi amfani da kudin a samar wa da jami’an kula da kiwon lafiyar jama’a ke bukata wajen yaki da cutar Covid – 19 da kuma taimakawa masu aiki a wurin cibiyoyin da aka killace masu fama da ciwon da kuma wuraren yi wa mutane Gwajin wannan cutar”.
” Musamman a samar da kayayyakin yaki da cutar da suka hadar da Sabulan wanke hannu, abin rufe baki da hanci, safar hannu irin ta Likitoci, Labarau iron na masu aikin Likita domin kariya da dai sauransu”.
” Kuma taimakawa mabukata irin haka zai iya samar da lada kamar irin yadda aikin Umara ka yi ko kuma ya ninnika samun Ladara ma baki daya”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.