Daga Imrana Abdullahi
Huzaufa Usman Usman samu nasarar kammala karatun nasa ne bayan da ya samu ainihin abin da ake bukatar samu a lokacin yin karatun na karatu da kuma na hali mai kyau kamar yadda yake kunshe a cikin kundin tsarin makarantar.
Da ga Sardaunan Badarawa ya zamo mai aikin yin taimakon jin kan jama’a ne da ya kasance ya sadaukar da kusan mafi yawancin lokacinsa wajen ziyarar gidajen marayu da yake taimaka masu da kuma yin taimakon marasa galihu a cikin al’umma a koda yaushe.
Za dai a iya cewa Huzaifa ya Gaji mahaifinsa ne da ya kasance shima Injiniya ne.
“Injiniya Huzaifa ya ci gaba da bayyana mahaifimsa a matsayin wani mutum mai kokari da hangen nesa da ke yin aiki tukuru domin ci gaban iyalinsa da kuma al’ummar kasa baki daya.
Injiniya Huzaifa Ibrahim ya kara jaddada cewa zai yi amfani da ilimin da ya samu wajen yin aiki tukuru domin gina Jihar Kaduna da kasa baki daya.
“Ina yi wa Allah godiya da farko da ya bani damar yin wannan karatu na aikin Injiniya
“Ina yin amfani da wannan kafar yada labarai domin nuna dimbin godiya ta ga mahaifina bisa irin taimakon da goyon bayan da ya yi Mani mara iyaka a duk lokacin da nake neman ilimi”.
“Ina neman taimakon Allah da bashi da iyaka musamman a halin yanzu da zai yi aiki da irin abubuwan da aka Koyar da ni a makaranta domin al’umma su amfana”, inji shi.