Daga Imrana Abdullahi
Alhaji Ibrahim Musa shugaban kungiyar masu shara da sarrafa karfafa ta kasa (NASWDEN) reshen Jihar Jigawa kuma mai magana da yawun kungiyar a arewacin Najeriya ya bayyana kungiyar su a matsayin wadda take aikin fadakar da matasa a kan su guji aikata abin da ba dai dai ba domin su dogara da kansu.
Hakan na taimakawa su taimaki kansu da iyayensu a bangaren karatu ko kuma a rayuwar yau da kullum ta yadda rayuwa za ta inganta.
Ibrahim Musa ya bayyana hakan ga manema labarai ne Jim kadan bayan kammala babban taron kungiyar inda aka Rantsar da sababbin shugabannin Jihar Kaduna da na shiyya da aka yi a Kaduna.
Ibrahim Musa ya bayyana shugabanni irin su tsohon Gwamnan Jigawa kuma babban Ministan tsaro a halin yanzu a matsayin shugabannin da ake bukata a halin yanzu wanda a sakamakon irin nasarar da muke samu a Jihar Jigawa sai shi da kansa ya sake rungumarmu ya ce shi ne Uban wannan kungiya. Kuma a halin yanzu wadansu sun mallaki kamfanin da zai fara sarrafa karfe, wato kamfanin “NAK” bisa hakan ne minista Badaru Abubakar ya hada mu da ministan Tama da karafa, don haka me meke cewa duk wanda ya duba tsari da tunani irin na ministan tsaron Najeriya a yanzu za a ga cewa ya na daya daga cikin wadanda ke ba Gwamnatin Najeriya dubunmawa ta yadda za a samu dai daituwar gwamnati Gwamnati samu ci gaba”.
Ibrahim Musa ya kara jaddada cewa matukar babban ministan tsaro na tare da shugaban kasa nan ba da jimawa ba kasar za ta canza baki daya, saboda kwakwalwarsa ta na bayarwa da kai sakon da ya kamata, kamar dai yadda na gaya maku masani ne a kan bunkasa harkokin tattalin arzikin kasa don haka duk hanyoyin da yakamata ya bi ya na bi domin inganta harkokin matasa a tarayyar Nakeriya sakamakon hakan ba abin da zamu gaya masa a duniya sai dai mu yi ta godiya kawai, Allah ya kiyaye shi ya martaba kujerarsa.
Alhaji Ibrahim Musa ya kara da cewa idan aka je Jihar Jigawa za a ga irin yadda kungiyarsu ta lakume kusan dukkan rabin matasan Jihar da suke ta gudanar da ayyukansu na yau da kullum a Jihar kuma suna dogaro da kansu.
“Kusan duk inda aka je a fadin Jihar Jigawa za a ga cewa matasa ne ke aiwatar da wannan sana’a mai albarka,kuma kasancewar wannan sana’a ta na taimakawa matasa a Jihar sai aka samu wani fasihin shugaba tsohon Gwamnan mu wanda a halin yanzu shi ne ministan tsaro kuma masanin tattalin arziki da na zamantakewa da ya lura da cewa harkar nan ta na tsaftace muhalli da kawar da kazanta da dukkan wani Datti ga samar da kudi mai yawa ta yadda matasa za su dogara da kansu, kuma a gefe daya har ma wata ma’aikata ce ake da ita ake ware mata kudi a kasafin kudi domin tsafta da kula da muhalli. Amma sai ga mu a kyauta muna tsafta ce muhallin kuma ana samar da ayyukan yi ga matasa sai kawai ya ga cewa wannan abu ne da ya dace ayi aikin hadin Gwiwa ta yadda duk shekara ko a wata idan sun kasance su dubu daya ne har sai su zama dubunnai, kuma da izinin Allah hakan aka yi wanda sakamakon hakan sai da mai girma tsohon Gwannan Jihar Jigawa ya yi yawo da mu kasashen duniya wanda ni din nan a kasar Cina na sayo jinjina daban daban har a yanzu muna sarrafa leda da kwalaye ana yin abubuwa daban daban har ana samar da kofunan shan ruwa da matasa da yawa ke samun hanyar abinci da damar gaske “.
“Kuma wani abin sha’awa ma a yanzu nan da nan sai kaga wannan matashin ya bude nasa can wancan ma ya bude a can ya sa jinjina ana taimakawa matasa.