…Yan Najeriya Sai Sun Tashi Tsaye
Daga Imrana Abdullahi
Jagoran kungiyar yan Arewa domin tabbatar da kyakkyawan shugabanci “Arewa movement for good Governance” Dokta Usman Bugaje ya bayyana Dimokuradiyya a matsayin wadda take a cikin mummunar matsala.
Dokta Usman Bugaje ya bayyana hakan ne a wajen wani taron manema labarai da aka yi a Kaduna
Dokta Bugaje ya ci gaba da cewa ta yaya shugabannin kungiyar yan majalisar Dattawan Arewa Arewa su yi shuru wasu shugaba da kakakin kungiyar yan majalisar Dattawan da suka fito daga arewa aka Jefa su a ciki duk da kokarin da suke yi na sai an tabbatar da gaskiya da adalci wajen batun tafiyar da kudin yan Najeriya musamman a cikin kasafin kudi.
Dokta Usman Bugaje ya ci gaba da cewa Najeriya na cikin wani hali na rushewa don haka ya na da kyau ayi abin da ya dace ta yadda za a tabbatar da yin gyara don gobe.
“Yawan kudin da ake kashe wa a wajen tafiyar da harkokin Gwamnati ya yi yawa domin kudin da ake kashe wa ba hankali a ciki a kasar da wasu mutane ke kwana ba su ci abinci ba kuma wadansu na mutuwa a asibitoci saboda kawai ba su da yan kananan kudin da za su biya asibiti”
Kamar yadda wannan kungiyar da nake yi wa shugabanci yake da muke tare da Kiristoci da musulmai ya nuna cewa dole sai an hada kai sannan a samu yaki da masu son rai da suke da dimbin hanyoyin bata kasa.
Saboda haka ne muke yin kira da babbar murya ga yan Najeriya da su kara kaimin tashi tsaye domin ganin wadannan yan majalisa ba su Kassara kasar ba.
Dokta Bugaje ya kuma lissafa wadansu abubuwa da yawa da ya ce suna da matukar muhimmancin gaske da ya dace a aiwatar da su domin samun kasar ta ci gaba, inda ya bayyana cewa A rufe dukkan akawun na Bankin da ake zargi, Matasa su tashi tsaye su kare gobensu sai kuma
Dole ne a matsayinmu na yan Najeriya mu tabbatar da wa muke zabe domin samun mutanen kirki su shugabanci kasar mu.
Kuma wani al’amarin da ya dace kowa ya lura da shi, shi ne irin yadda ake a wannan kungiya mai kokarin a samar da kyakkyawan shugabanci akwai musulmi da Kirista duk saboda mun fahimci lallai sai mun hada kai ta yadda za mu hana baragurbin yan siyasa su Kassara mana kasa domin duk abin da suke yi son zuciya ne kawai ta yadda za a samu wata biyan bukata ta kashin kai kurum.
” ta yaya za a ce wai dan majalisa zai Sanya a cikin kasafin kudi wai za a yi aikin turken samar da hasken wutar lantarki mai aiki da hasken rana guda daya kawai a kan makudan miliyoyin naira? Ko kuma wani dan majalisa ya Sanya a cikin kasafin kudin ayyukansa da zai yi shi da yake an zabe shi daga wata mazaba a Kudancin Najeriya amma ya yi aikin mazaba irin na dan majalisa a Sakkwato?
Don haka dole sai yan Najeriya sun tashi tsaye domin kada yan son zuciya su Kassara mana kasa baki daya, musamman sai an tashi tsaye wajen fadakar da jama’ar kasa mutanen da ya dace a zaba a duk lokacin zabe idan yazo.