Home / Labarai / Allah Ya Kawo Mana Karshen Matsalar Tsaro Da Tsadar Abinci – Husaini Jalo

Allah Ya Kawo Mana Karshen Matsalar Tsaro Da Tsadar Abinci – Husaini Jalo

Daga Bashir Bello  Dollars, Kaduna
Honarabul Husaini Muhammad Jalo, dan majalisa ne mai wakiltar mazabar karamar hukumar Igabi a majalisar wakilai ta kasa ya yi addu’ar albarkacin Azumin watan Ramadana da musulmi suka yi Allah ya kawo karshen matsalar rashin tsaro da tsadar abincin da ake ciki.
Honarabul Husaini Muhammad Jalo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.
Honarabul Jalo ya ci gaba da cewa hakika ana cikin wani hali na tsadar abinci da batun rashin tsaro wanda hakan ya rutsa har da mazabarsa ta karamar hukumar Igabi, da ya fayyace cewa matsalar tsaron ta yi yawa kwarai a yan kwanakin nan.
” Muna yi wa Allah mai kowa mai komai godiya da ya raya mu har muka ga karshen watan Azumin Ramadana da aka kammala, dukkan alkairan da ke cikin watan Allah ya tabbatar mana da shi kuma ina yi wa mutanen mazabata,Jihar Kaduna da Najeriya baki daya fatan Alkairi, ina kuma yin addu’a ta musamman a game da halin kuncin da jama’a ke ciki na rashin kudi da abinci Allah ya yaye wa kowa ya kawo karshen lamarin da kuma irin kashe kashe da satar jama’a da ke faruwa a musamman mazabata ta Igabi lallai ya yi yawa muna fatan albarkar wannan watan da muka yi Azumi Allah ya kawo karshen wadannan fitintunu baki daya

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.