.…Za A Bude Dakin Karatu A Majalisar Kasa
Bashir Bello majalisa Abuja
Sanata Rufa’i Sani Hanga ya bayyana cewa a majalisar Dattawa sun zauna sun tattauna abubuwan da za su ciyar da kasa gaba da yawa domin amfanin kasa da jama’arta baki daya.
Sanata Hanga ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Abuja.
Hanga ya ce akwai yan kishin kasa da dama da suka hada da lauyoyi da dimbin yan Gwagwarmaya duk an tattauna abubuwan da za su amfani kasa da nufin samun mafita da ci gaba.
“Duk sun zo sun kuma kawo ra’ayinsu a kai, domin daman waccan da aka kawo Sojoji ne suka kawo ta kuma ba ta dace da mu ba sam. Da suka kawo wannan sai suka cire ta asali da za ta kawo zumunci da yan uwantaka its ce ta da can ana girmama Najeriya kassr mu kuma ta na cewa mun dogara da yan uwantaka kuma za mu zama yan uwan Juna ba za a zalunci kowa ba domin ba zalunci a tsarin don haka abin da waccan ke fadi kenan. Amma wannan kawai domin wani dalili ne na soja da ya kawo ta saboda kishin kansa ko domin ya na jin haushin wannan ta da ne ko dai domin wani dalilinsa ne ba mu Sani ba don haka ne aka kawo shawarar cewa yakamata a canza ta an kuma bi duk wasu hanyoyin canza doka da a yau ne aka kawo karshen ta baki daya.
“Kuma a gobe za a kaddamar da dakin karatun da muka gina a majalisar Dattawa da kuma za mu shiga cikin Jirgin kasan da aka samar da zai rika yin jigila a cikin Abuja duk domin bikin ranar Dimokuradiyya”, inji Sanata Hanga.