Home / Uncategorized / Matawalle Bashi Da Alaka Da Bashir Hadeja – Suleiman Shinkafi

Matawalle Bashi Da Alaka Da Bashir Hadeja – Suleiman Shinkafi

Tsohon mai ba  tsohon Gwamnan Jihar Zamfara shawara a kan harkokin kasashen waje da yarjejeniyoyi Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya ce babu wata alaka tsakanin tsohon Gwamnan da Bashir Hadeja.

Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai

 “Wallahi tallahi abin ya na bani mamaki irin yadda wasu jaridu da ba theshield ko Garkuwa ba suka rubuta cewa wai wani maitaimakawa Matawalle da ake kira Bashir Hadeja da suke zarginsa da batun safarar makamai da Sumogal.

Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi sai ya ce abin da ke ba ni mamaki shi ne, abin da ku yan jarida zaku tabbatar shi ne wallahi tallahi babu inda halakar wannan mutum ta hadu da Matawalle ko fa Matawalle ya gani zai iya yanka shi, to, ta yaya za a ce alakarsa ta hadu da Matawalle?

Ya ci gaba da bayanin cewa ya dace ayi wa mutum adalci domin suk wanda ya san Bashir Hadeja ya san ya na da kiyayya da Matawalle kuma ko a lokacin zaben da ya gabata a Jihar Zamfara Bashir Hadeja na daya daga cikin wadanda suka cuce mu suka Yaudare mu suka haifar mana da faduwa zabe”.

Kuma, ” Ai ba mataimakin Matawalle ba ne ta ina ya zama mai taimaka masa, saboda haka muke yin kira ga jama’a da duk abin da za a yi lallai ayi adalci kuma wadannan jaridun da suka wallafa wannan rubutun lallai su jaye wannan magana ko kuma mu yi karar su domin shi ba mai taimakawa Matawalle ba ne shi ba Aminin Matawalle ba ne asalima shi makiyin Matawalle ne domin bai son Matawalle an dai saka wannan suna ne kawai domin kawai ba ta suna.

” Muna son duk duniya ta san cewa Matawalle bashi da alaka Bashir Hadeja, amma aka ce wai Matawalle Aid Arrested saboda Allah ta yaya har bashir   Hadeja ya zama mai taimakawa Matawalle da yaushe kuma a ina

“An dai kama shi can domin na san DSS ba za su kama mutum haka kawai bai yi laifin ba sai sun tabbatar da laifinsa kuma sai sun dade suna bibiyarsa, to, ina ruwan biri da Gada, ina ruwan Matawalle da Bishir Hadeja, mu a iya sanin mu shi ne Bishir Hadeja makiyin Matawalle ne kuma ba mu da alaka da shi Sam domin ba mu ko san shi ba baki daya don haka idan ya yi laifi a kama shi a kuma hukunta shi amma ba wata alaka da Matawalle.

Dokta Shinkafi ya ci gaba da cewa ya na bukatar lallai jaridun da suka wallafa da suka hada da Sahara Reporters su cire sunan Matawalle dole ne fa mutane su ji tsoron Allah a kuma yi adalci ta ina kuma a yaushe aka dauki Bashir aiki, idan akwai to a kawo takardar da aka dauke shi aiki , mun yi Allah wadai da irin wannan mun kuma yi Allah wadai da batun baki dayansa, domin wallahi bashi tare da Matawalle kuma baya son Matawalle Sam ya dai yi Allah wadai da lamarin.

“Muna yin kira da babbar murya duk wanda ya aikata laifi a kama shi a yi masa hukuncin da ya dace kawai hakan ne matsayar mu”.

Don Allah ku daina yada wannan domin mun san cewa mune masu aikin taimakawa Matawalle ba irin su Bashir ba . ” zan kai Sahara reporters da jaridar da ta buga wannan labarin kage Kotu, mun nesanta kan mu da wannan batu ba mu ba ku ko kadan , muna kuma son yan Najeriya su Sani cewa wannan duk bita da kulli ne kawai sharri ne da Kage kawai

About andiya

Check Also

Bafarawa Ya Kaddamar Da Kungiyar Matasa Domin Ceton Arewa Da Najeriya Baki Daya

….Mu Bamu da wata matsala da kowa, inji Bafarawa Imrana Abdullahi A wajen wani babban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.