Home / Uncategorized / Mun Gabatar Da Rahoto A Kan Al’amuran Yan Sanda A Najeriya – Honarabul Yalleman

Mun Gabatar Da Rahoto A Kan Al’amuran Yan Sanda A Najeriya – Honarabul Yalleman

Muna addu’ar Allah ya gafarta wa wadanda hadarin tamkar mai ya shafa a Jigawa 

Bashir Bello Abuja

Dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar kananan Hukumomin Malamadori da Kaugama a majalisar wakilai ta kasa Honarabul Maje Abubakar Yalleman, ya bayyanawa manema labarai cewa bayan tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki a kan harkokin yan Sanda a yanzu kwamitin ya Gabatarwa majalisa da ainihin rahoton da suka tattara

Za kuma a tattauna batun a gaban majalisa domin samun mafita a kan batun Yawan shekaru da abin da ya dace yan Sanda su yi a Najeriya idan suna bakin aikinsu na harkar tsaro.

“Masu ruwa da tsaki a kan harkokin yan Sanda kowa ya tofa albarkacin bakinsa kuma a matsayinsu na yan kwamiti duk sun hada komai a guri daya a rubuce, an kuma ajiye a gaban majalaisa”.

A game da batun irin matsalar iftila’in da aka samu a Jihar Jigawa da aka rasa rayuka sakamakon hadarin wata Tankar Mai kuwa sai Hon Maje Abubakar Yalleman, sai ya ce hakika ba a taba samun irin wannan iftila’in ba a Jihar, amma dai daga Allah muka fito kuma daga gare shi za mu koma kuma kowa ne dan adam da ya kasance a raye ya na da silarsa komawa ga mahaliccinsa don haka sai dai kawai ayi addu’ar Allah ya jikansu baki daya da rahama, wadanda suka jikkata Allah ya ba su lafiya.

“A gurguje ma Gwamnan Jihar yaje wurin da lamarin ya faru ya kuma gani da idanunsa kuma nima a yau a majalisa da sahalewar dukkan yan uwana mu tashi mu yi masu addu’a Allah ya gafarta masu a mutuwar shahadar da suka yi marsa lafiya kuma Allah ya ba su lafiya”.

” Gwamnan Jihar Jigawa yaje wurin da kansa ya kuma kai masu saukin gaggawa na wadanda suka ra su da kuma wadanda suka samu rauni a wurin kuma har an yi Jana’iza tare da shi bayan nan ma Sanata n da ya fito daga yankin Babangida Usaini ya gabatar da kudiri a gaban majalisa kuma har ya nemi Gwannatin tarayya ta kawo dauki ga mutanen da lamarin ya shafa

About andiya

Check Also

Dangote Hails Tinubu on Impact of Crude for Naira Swap Deal

      …As Dangote Refinery partners MRS to sell PMS at N935 per litre …

Leave a Reply

Your email address will not be published.