Wani mai gwagwarmayar kwato yancin al’ummar kasa da kuma fadakar wa Bashir Nafaru ya bayyana irin halin Kuncin rayuwar da jama’ar Najeriya ke cikin da cewa wani lamari ne da ke bukatar kara yin addu’ar neman saukin daga Allah madaukakin Sarki.
Bashir Nafaru ya ce halin da ake ciki fa a yanzu shugabancin da muke ciki ne a yanzu ya Jefa kasar a cikinsu. Kuma idan an duba irin yadda sakataren Gwamnatin tarayya da ya fito yana cewa sai a bari kawai har sai mai gidan nasa a yanzu ya kare Mulkinsa na 2031 saboda haka wallahi a kasar nan muna cikin matsala kwarai”.
“A lokacin da wannan mutum ya karbi mulki a can baya litar Mai ana sayar da ita 175 ko185 ake sayar wa a wadansu gidajen mai, amma a halin yanzu litar mai ana sayar da ita naira dubu daya da dari biyu har da dari Uku 1200 har 1300 duk ana sayar da litar mai a yanzu don haka ne mu a halin yanzu mun bar wa Allah zabi kuma muna yin addu’ar idan wani laifi muka yi maka Allah ka yafe mana ka kawo mana wanda zai Ceci kasar nan kuma muna rokon Allah duk wanda ya fi zama alkairi idan PDP,AD,Afga ko duk wace jam’iyya ce alkairi da za su taimaki al’umma Allah ka kawo mana su a halin da ake ciki ne a yanzu da kayi tafiya idan ka dawo ka da san wannan mutum na cikin kamarsa amma a yanzu sai kawai ka rika tambaya ko wanene domin ka kasa gane shi Sam muna rokon Allah ya kawo mana canjin Gwamnati mai albarka shugabanni masu albarka, Allah ka kawo mana mutanen kirki a cikin kasa baki daya