Home / Uncategorized / Yin Amfani Da Kayan Noma Da Aka Samar Wanda Babu Kemical Zai Magance Matsalar Noman Citta – Gagarin Madaki

Yin Amfani Da Kayan Noma Da Aka Samar Wanda Babu Kemical Zai Magance Matsalar Noman Citta – Gagarin Madaki

 

An Gano Magajin Matsalar Cutar Da Ke Addabar Gonakin Citta A Kaduna

 

Daga Imrana Abdullahi Kaduna

 

Shugaban kungiyar masu Noman Citta a tarayyar Najeriya Mista Gagarin Madaki, ya bayyana cewa yin amfani da kayan Noman da aka samar da babu wani Kemican ( Organic) a cikinsu zai taimaka wajen yin maganin matsalar da manoman Citta ke samu a Gonakinsu saboda haka wannan hanya ita kadai ce mafita ga manoman Citta a Najeriya.

 

 

Gagarin Madaki ya kuma tabbatarwa manema labarai a Kaduna cewa yin amfani da wannan hanyar na cikin abin da tsarin Noma na kasa da kasa ya amince da shi.

Indai zaku iya tunawa manoman Cutta a Kaduna sun yi fama da matsala a shekarar da ta gabata wanda dalilin hakan aka samu asarar da ta kai sama da biliyan Goma, sakamakon wata cuta da ta kama Gonakin Citta a Jihar.

Da yake yi wa mahalarta babban taron kaddamar da maganin wannan cuta ga manoman Citta da suka taru a dakin taro na Otal din NAF da ke cikin garin Kaduna, domin kaddamar da abubuwa guda biyu da aka samar don Citta da kuma Tumerik, wanda zai magance waccan matsalar da aka samu.

Madaki ya ce bayan an gudanar da bincike na a kalla shekaru 10 a game da Noman Citta, an duba irin kalubalen da ke samun Noman Citta, sai aka yanke shawarar samar da wata mafita musamman ga manoman Citta.

Ya ce daga irin kwajin da aka yi a wannan shekarar, an gano cewa za a iya yin Noman Citta ta hanyar yin amfani da irin wannan kayan Noman da aka samar ba tare da kemikal ba ko kadan da ake samun komai a nan gida Najeriya don haka an samu mafita kenan daga matsalar da aka samu a shekarar da ta gabata game da Noman Citta a Jihar Kaduna.

“Ta hanyar amincewa da yin amfani da wannan hanyar yin amfani da sabuwar hanyar Noman Citta ta yin amfani da kayan Noman da babu sinadarin kemikal, hakika na tabbatar da cewa za a iya samar da amfanin Gona mai inganci da kasa da kasa suka amince da ita”. Inji Gagaren.

Sai ya kuma bayyana jin tsoronsa saboda irin matsalar da Citta ta samu a Gonaki a shekarar da ta gabata, manoma da dama sun ja baya da yin Noman Citta a wannan shekara, sai ya kara cewa daga bangaren kungiyarsu, sai suka yi koyi da irin yadda iyaye da kakanni suka yi Noma ta hanyar yin amfani da Takin gargajiya da nufin inganta al’amura.

Shugaban kungiyar na kasa ya kara jaddada cewa yin amfani da wannan hanyar ta yin amfani da kayan Noma mara sinadarin kemikal zai kasance abincin da za a Noma mai inganci da lafiya a koda yaushe.

 

 

Sai ya bayyana damuwarsa a game da irin yadda Noman Citta Citta samu matsala a shekarar da ta gabata, wanda hakan ya sa manoma da dama sun ja baya saboda irin asarar da suka yi

Ya ce daga bangaren kungiyarsu dole ne suka yi aiki tare da wadansu manoma kalilan domin yin amfani da irin hanyar gargajiya ta iyaye da kakanni da suka yi amfani da ita wajen Noman Citta ta hanyar yin amfani da Takin gargajiya daga Dannobi da kuma Bolar da ake zubarwa ana saran samun amfani sosai a wannan shekarar.

 

Shugaban kungiyar Noman Cittan na kasa sai ya ci gaba da cewa yin amfani da wannan hanyar kayan Noma da babu sinadarin kemikal a cikinsa ba wai zai yi wa manoman Citta kawai ba ne amfani amma har da kara inganta yanayin kasar Noman Noman ake amfani da ita kuma akwai fa’ida kwarai da za a samu wajen Sayar da kayan Noman da aka yi amfani da wannan kayan Noman da aka samar a cikin gida mara sinadarin Kemikal, domin Ko a kasashen waje ana bukatar kayan Noman da babu sinadarin kemikal a cikinsu don haka ana samun makudan kudi fiye da kayan Noman da aka Sanya wa sinadarin kemikal a wurin Noman.

Tun da farko Farfesa Alimi Olasunkanni Maruf, na cibiyar ilimin kere kere a rundunar sojojin Sama da ke Kaduna, cewa ya yi akwai bukatar manoman Citta da sauran kayan Noma su hada kansu su taru wuri daya da nufin samar da mafita ga kalubalen da ke fuskanta harkar Noma a bangarori da dama a Najeriya.

Ya ce manoma ya dace su Sani cewa za su iya kara karfafa abin da suke samu kuma su daina yin amfani da tsohuwar hanyar da ake amfani da ita ta hanyar yin amfani da Kemikal da ke da matsala ga lafiyar jama’a da kuma cutar da kasar Noma baki daya.

Wannan ne babban wurin zaman manyan bakin da suka halarci taron kaddamarwar a kaduna

Sai ya shawarci gwamnati a kowane irin mataki da ta yi amfani da wannan kyakkyawan binciken da aka yi domin kara bunkasa Noma a kowa ne fanni a Najeriya baki daya.

Shugaban al’ummar Yarbawan Jihohin arewacin Najeriya Goma sha Tara (19) da Abuja babban birnin tarayya, Oba kuma Cif Muhammed Arigbabuwo, kira ya yi ga masu ruwa da tsaki da su rika bayar da muhimmanci ga abubuwan da ake samar wa a cikin gida ta hanyar amfani da ilimin kimiyya da fasaha,a kuma taimakawa abin da zai samar da warware dukkan wata matsalar da ake fuskanta a bangaren ilimi,Noma da matsalar rashin aikin yi ga matasa.

Ya kuma ce Farfado da masana’antu da kuma bayar da bashin da babu ruwa a cikinsa zai samar da ci gaban da ake bukata a cikin kasa.

About andiya

Check Also

Northwest PDP Youth Leader Atiku Yabo Commends Hon Mai Kero Of Kaduna South For A Job Welldone

      The people Democratic Party Northwest Youth leader Alhaji Atiku Muhammad Yabo has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.