Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Sanata Abdul’Aziz Yari Abubakar, da ke wakiltar Zamfara ta Yamma ya jajantawa al’ummarsa da ke wadansu kauyuka a karamar hukumar Matadun a Jihar Zamfara bisa aka kashe bisa kuskure sakamakon kokarin da ake yi domin tarwatsa yan bindiga.
Duk da dai yawan alkalumman wadanda lamarin ya shafa har yanzu ba a fitar da su ba, Sanatan ya yi kira ga daukacin al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da yin addu’a ga Allah madaukakin Sarki da ya amshi Shahadarsu wadanda suka rasu ya Sanya su a cikin Aljannah Firdausi
Sai ya mika ta’aziyyar sa ga iyalan wadanda suka rasu ya kuma yi addu’ar Allah ya kiyaye afkuwar hakan nan gaba, da addu’ar Allah ua ba wadanda suka samu raunuka sauki da waraka.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da ke dauke da da hannun Darakta Janar mai kula da kafofin yada labarai na Sanata Abdul’Aziz Yari Abubakar, shugaban kwamitin ruwa na majalisar Dattawa Najeriya.
Sanatan ya kuma yi addu’ar Allah ya ba jami’an tsaron soja nasarar kakkabe duk wani aikin batagari masu haifarwa da jama’a matsalar tsaro, muna kuma yin kira da a dauki matakan da suka dace a nan gaba domin gujewa faruwar abin da ya faru a yanzu, Allah ya kara kawo mana ci gaba da samun zaman lafiya da karuwar arziki.