Home / Uncategorized / Kungiyar Zamfarawa Mazauna Kaduna Sun Tallafawa Mutane 280

Kungiyar Zamfarawa Mazauna Kaduna Sun Tallafawa Mutane 280

 

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna

 

 

A kokarin da hadaddiyar kungiyar da ta gama kan dukkan al’ummar Zamfarawa mazauna Kaduna take yi na ganin rayuwar Mutanensu ta kara inganta ya sa suka yi wani babban taro a garin Kaduna inda suka bayar da tallafi tare da nuna shugabannin kungiyar.

 

 

Kamar dai yadda shugaban kungiyar ya fadi a wajen taron Dokta Abubakar Liman Shinkafi, ya ce wannan taro ne na shekara domin kaddamar da bayar da kudi naira dubu Hamsin gamutane 280 da suka kasance yan asalin Jihar Zamfara da suka fito daga kananan hukumomi 14 da nufin su bunkasa sana’o’insu ta yadda kowa zai samu dogaro da kansa.

Dokta Abubakar Liman Shinkafi ya ci gaba da fayyace cewa akwai muhimman dalilai guda hudu da suka Sanya aka kafa wannan kungiyar da suka hada da na farko, samun hadin kai da zumunci, kamar dai yadda musulunci ya yi Umarni ayi domin tun lokacin da muka fara yin wannan kungiya akwai wasu a yawa da sai a lokacin suka ga Juna kuma suna mamaki har suna cewa wane kana nan ashe?

Sai na biyu a taimakawa Juna kasancewar Allah bai yi mu duk daya ba a cikin al’umma? Kamar yadda Allah ya ce ya bambance mu da ban daban, saboda haka wannan da aka fara kadan ne akwai tsare tsare masu yawa na Tallafawa mutane mabukata.

Abu na Uku shi ne taimakawa Gwamnatin jihar Zamfara kowa ke mulki zamu taimaka masa domin duk wanda ka gani hankalinsa na Zamfara duk abin da ya faru na matsalar tsaro ba mu jin dadi amma da an samu sauki sai mu ji dadi saboda haka duk abin da za mu yi mu bayar da gudunmawa ga Gwamnatin jiha tun daga addu’a da ziyara da nufin samun ci gaban Jihar mu mai albarka.

Haka kuma makasudi na hudu shi ne mu bayar da gudunmawa ga Gwamnatin jihar Kaduna mai masaukin mu domin wasu sun zo ne ta hanyar aiki, wasu ta hanyar Zumunci, wasu sun zo ne ta hanyar gudun hijira saboda haka za mu bayar da gudunmawa ga Gwamnatin jihar Kaduna.

“Saboda haka don my cimma abin da muka Sanya a gaba mun kafa Kudirori guda Takwas akwai kwamitin kulawa da ayyukan kungiya daban daban wato,”central working committee”, sai kwamitin kulawa da bayar da tallafin karatu, kwamitin kulawa da matasa da ci gabansu, domin nemawa matasa ayyukan yi, kwamitin kulawa dayan kasuwa da kasuwanci, kwamitin kulawa da ayyukan jin kai domin Tallafawa jama’a, wanda .a karkashin kwamitin ne ake yin wannan aikin a yau cikin yardar Allah sai kwamitin sanar da jama’a ayyukan kungiya da wayar da kan jama’a da hulda da yan jarida sai kwamitin kulawa da kudi da ayyukan kudi sai kwamitin kulawa da zaman lafiya da tsawatawa da kuma sasanta tsakanin jama’a kuma duk za su fara gudanar da ayyukansu nan gaba kadan za a ga amfaninsu.

 

 

Shugaban kungiyar ya ci gaba da cewa, “Dalilan kafa wannan kungiya kamar yadda shugaban ya bayyana wa taron jama’ar da suka halarci taron mikawa mutane 280 kudin tallafin da aka ba su inda ya ce ” duk an yi wannan tunani ne na samar da wannan kungiya mai rajista ta kasa da hukumar yin rajista ta Gwamnatin tarayya don akwai satifiket din rajistar duk an yi ne domin inganta rayuwar jama’a masu karfi da marasa karfi a ta fi tare a cikin harkokin rayuwar duniya.

Sai dai shugaban kungiyar ta Zamfarawa mazauna Kaduna Dokta Abubakar Liman Shinkafi, ya ce saboda rashin samun isassun kudin da suke bukata na naira miliyan Goma sha hudu kamar yadda suka tsara da za a iya ba mutane 280 kudi naira dubu Hamsi a yanzu sun samu kudi ne sama da miliyan Goma wanda kudi ma fi yawa na naira miliyan Goma suka fito daga Honarabul Abdulmalik Zubairu, Zannan Bungudu sai kuma wadanda suka bayar da wadansu kudade don haka duk lokacin da aka samu kudi lallai za a kira mutane a cika masu dubu Ashirin kamar yadda aka tsara tun farko domin kowa ya ci gaba da sana’arsa da yake yi”.

Taron dai ya samu wakilcin mutane daga Gwamnatin jihar Kaduna wanda mai ba Gwamnan Kaduna shawara da kuma Hajiya Rabi Salisu kwamishiniyar ma’aikatar kula wa da ayyukan jin kai ta Jihar Kaduna da Waziri Gusau Alhaji Bala Abdullahi da dai dimbin jama’a daga Jihar Kebbi da Kaduna duk sun samu halartar babban taron.

Babban abin farin ciki dai daya faru a wajen taron shi ne sai da aka rabawa kowa ce karamar hukuma inda aka kira kowa ne da ya amfana da suka hada da Maza da Mata kudi naira dubu Talatin nan take, kowace karamar hukuma mutane 20 suka amfana.

About andiya

Check Also

Call Your Wife To Order, Niger Delta Groups Warn Uduaghan, Husband Of Senator Natasha

    ..Say outburst against Senate President Akpabio, shameful, unwomanly A coalition of groups from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.