Bafarawa ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ta ɓulla a yau Talata 14 ga watan Janairun 2025, wadda ya sanya wa hannu da kansa.
A cikin wasiƙar ficewa daga jam’iyyar, wadda ya rubuta wa shugaban jam’iyyar na ƙasa a ranar 8 ga watan Janairu, Bafarawa ya ce: “Na rubuto wannan takarda domin gabatar da matakin ficewa daga jam’iyyar PDP”.
Ya ƙara da cewa “duk da cewa wannan ba mataki, wanda na ƙashin kaina ne kuma ba mai sauƙi ba, na ɗauke shi ne sanadiyyar mayar da hankalin da na yi kan wani sabon babi na aiki daban wanda ya yi daidai da manufata ta bunƙasa al’umma ta hanyar ƙarfafa matasa.”
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ta PDP ke fama da matsaloli sanadiyyar rikice-rikicen shugabanci da kuma saɓanin ra’ayi na cikin gida.
Kwana daya kafin bayyana takardar ficewar Bafarawa daga jam’iyyar ta PDP, wasu ƴaƴan jam’iyyar sun gudanar da zanga-zanga a babban ofishinta da ke Abuja, sanadiyyar wata harƙalla kan sahihin sakataren jam’iyyar na ƙasa.
Lamarin da ya zo bayan tsawon watanni da aka kwashe ana taƙaddama kan shugabancin jam’iyyar, wanda ake ganin gurbi ne na yankin arewa ta tsakiyar Najeriya, a maimakon halin da ake ciki yanzu inda shugaban jam’iyyar, Umar Damagum ya fito daga arewa maso gabas.
Duk da cewa PDP ita ce babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, ana ganin cewa rikice-rikice na cikin gida ya yi mata tarnaƙi, ta yadda ba ta iya sauke nauyin da ke kanta na sanya ido kan lamurran gwamnati mai ci ƙarƙashin jam’iyyar PAC.