Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya hori Jami’an yada labarai na Ma’aikatun Jihar da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukan su cikin nutsuwa.
Gwamnan Wanda sakataren gwamnatin Jihar Alhaji Baba Malam Wali ya wakilta ya bayyana hakan ne a yayin bude taron bita na kwanaki uku kan sanin makamar aiki ga jami’an yada labarai na ma’aikatun gwamnatin Jihar wadda kwamishinan ma’aikatar yada labarai, cikin gida da al’adu Alhaji Abdullahi Bego ya shirya da aka gudanar a dakin taro na otal din CEDARS da ke Damaturu .
Gwamnan ya bukaci jami’an yada labarai da su jajirce wajen ganin sun gudanar da ayyukan da al’ummar jihar Yobe za su amfana.
Ya jaddada muhimmancin gyara bayanai, bisa la’akari da jawabin da gwamnati ta yi a can baya wajen aiwatar da aikin jami’an, hakan ya sanya gwamnati ta ware wayoyin hannu (Smart phones) da kwamfutar tafi-da-gidanka (Laptops) ga jami’an yada labarai na gwamnati don kula da ayyukan su yadda ya kamata.
A nasa jawabin ya yn bude taron bitar, kwamishinan ma’aikatar harkokin cikin gida, yada labarai da al’adu, Abdullahi Bego ya bayyana irin cigaban da aka samu dangane da yadda aka shirya irin wannan taron bitar da aka yi a baya, ya bada tabbacin cewa mahalartan za su kara kaimi tare da yin aiki bayan samun karin wannan horon a yanzu.
Bego ya kuma jaddada cewa, bada kyawawan bayanai wani muhimmin abu ne da ke daidaitawa da samar da hadin kai tsakanin gwamnati da jama’ar jihar.
Wadanda suka halarci taron suka kuma bada gudummawar su da bayanan su a wannan taron bita sun hada da, Farfesa Abdullahi Bashir, Jami’ar Abuja, Farfesa Danjuma Gambo Jami’ar Maiduguri, Dr. Musa Usman, Dr, Rukaiya Yusuf da sauransu.