Daga, Sani Gazsa Chinade, Damaturu
Akalla mutane bakwai ne suka mutu sannan goma sha daya suka jikkata a wani hari da ‘yan fashi da makami suka kai a kasuwar Ngalda da ke karamar hukumar Fika a jihar Yobe.
Wadannan ‘yan fashi da makamin dai sun kai harin ne don sace dukiyoyin mutane a yammacin ranar litinin a daidai lokacin da kasuwar ke shirin tashi.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan bindigar da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun bude wuta kan ‘yan kasuwa da masu shaguna, lamarin da ya haifar da firgici da hargitsi.
A halin da ake ciki gwamna Buni ya jajantawa iyalan wadanda suka mutu tare da jajantawa wadanda suka jikkata.
Ya kuma umurci gwamnatin jihar da ta bayar da tallafi ga iyalan wadanda abin ya shafa.
Gwamnan ya kuma umarci hukumomin tsaro da su binciki musabbabin lamarin tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kuliya don girbar abin da suka shuka.
“Ya kamata ku yi cikakken bincike, ku binciki irin hanyoyin da za a bi don kiyaye afkuwar irin ya hakan nan gaba, ” inji Gwamna Buni.
Kasuwar Ngalda ita ce babbar kasuwar dabbobi a yankin, inda ake samun ‘yan kasuwa daga jihohin da ke makwabtaka da su na zuwa domin saye da sayarwa.