Daga Imrana Abdullahi
Hukumar horas da al’ummar Najeriya sana’o’in dogaro da kawunamsu ta NDE na kokarin ganin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu tare da gwamnatin da yake yi wa jagoranci sun cimma birin kudirorin da suka sanya a gaba domin kasa ta ci gaba da bunkasa.
Shugaban hukumar NDE ta kasa Darakta Janar Silas Ali Agara ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala bikin ranar hukumar a kasuwar duniyar kasa da kasa da ke Kaduna karo na 46 da ke ci a halin yamzu a Kaduna.
Mista Silas Agara ya ci gaba da bayanin cewa, “su a hukumat NDE ta kasa za su iya taimKawa ta hanyar kouawa jama’a sana’o’in da kowa zai dogara da kansa ta yadda shigaban kasa zai samu sukunin cika alkawuran da ya yi wa jama’a a game da kudirorinsa, a wannan hukuma ta NDE shi ya sa aka yi canji kadan domin kwalliya ta biya kudin sabulu kasa baki daya ta samu ci gaba.
Darakta janar din ya kara da cewa a halin yamzu samun damar shiga koyon sana’o’i a hukumar NDE ba sai mutum ya san wani ba ko an bashi wata takarda ba, kawai mutum zai iya yin rajista da kansa a dandalin NDE za kuma a nemi mutum domin yin duk abubuwan koyarwa da ake yi a NDE.
“Muna yin amfani d wannan damar mu sanar da jama’a cewa ba sai lallai mutum ya tashi daga inda yake ba yaje Legas ko Kano domin yin ayyuka ko abubuwan da mutum zai samu wani amfanin da ya dace ya samu a rayuwarsa ba kowa zai iya samun amfani ba tare da ya haifatwa da kansa wata matsala , rayuwa a yanzu ta canza mutum zai iya zama a Kaduna kuma ya yi aiki a Legas, mutum ya zaina a Kaduna kuma ya bayar da amfani a Amerika a halin yamzu irin yadda abubiwan ke tafiya matasa na yin aikin da ake biyansu a dola ba ma a Naira ba don haka a halim yanzi lokaci ya yi da yara za su nemi aikin da yakamata ba kawai mutum ya yi karatu ya ce sai ya samu takatdar shedar da zai yi aiki da ita ba tukunna”.
“Ko a cikin rumfar NDE da ke wannan kasuwar duniya akwai wata yarinya da ta kammala aikin hidimar kasa kuma a yau ta na da shagon yin takalma kuma ta gamsu da abin da hukumar NDE ta koya mata a koda yaushe ta na jin dadi sosai don haka irin abubuwam da NDE Keston yi wa matasa kenan, kunga mitane na yin aikin hannu duk da sun kammala karatun boko amma suna da sana’ar hannu don haka mai sana’ar hannu ko mace ce za ta iya yin sa kuma a kawo amfani a gidan