Related Articles
….Datakta Janar na hukumar kula da ingantuwar ayyuka, Dokta Baffa Babba DanAgindi, ya bayyana cewa mutane dugu Goma Sha biyar (15000) ne za su amfana daga wannan hukumar
Abdulmajid Dan Dawaki, mai bayar da shawara ne na musamman ga Darakta Janar na hukumar kula da iangantiwar ayyuka ta kasa Dokta Baffa Babba Dan Agundi, ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da wakilinmu jim kadan bayan kaddamar da yabon Fom ga kungiyoyin da za a ba su kudi kyauta daga hukumar.

Dan Dawaki ya ci gaba da bayanin cewa a kokari irin na Dokta Baffa Babba Dan Agundi, mutane akalla dubu Goma sha biyar ne za su amfana daga shiyyar arewa maso Yamma da suka hada da jihohin Kano, Jigawa, Katsina, Kaduna, Sakkwato, Zamfara da Kebbi.
“Wannan tallafin da za a bayar ga jama’ar da aka san lallai sun yi aiki sun wahala da tafiyar harkokin siyasar Gwamnatin APC saboda babu wanda za a bari a baya duk wanda a ka sani na cikin tafiyar APC Ciki Da Waje wadanda aka sani suna cikin gamayyar kungiyoyin da suka yi wa APC aiki la shakka za su amfana da dimbin abubuwan da aka tanadar domin a raba”.
Sai Dan Dawaki ya yi kira ga daukacin mutanen da aka nada a kowane irin mukami ko aka zabe su a kujeru daban daban da su yi ko yi da irin abubuwan ci gaban al’umma da Dokta Baffa Babba Dan Agundi yake yi daga hukumar da aka ba shi jagoranci ta ingantuwar ayyuka da aka fi sani da ( national Ptoductivity Center).
“Hakika da a arewa mado Yamma za a samu mutane kamar Dokta Baffa Babba Dan Agundi kamar mutum biyar zuwa Goma da aka nada su mukamai na Gwamnatin tarayya da an samu ci gaban jam’iyyar APC, yankin da jama’arta baki daya kuma da babu wata jam’iyyar da za a rika koda ambatonta baki daya a kasa Najeriya don haka lallai ayi ko yi da Baffa Babba Dan Agundi a ayyukan da yake yi”.
Da yake tofa albarkacin bakinsa shugaban gamayyar kungiyoyin da suka yi wa gwamnatin APC a lokqcin zabe da ake kira ( APC Support Group) Musa Bawa FCNA cewa ya yi a matsayin sa na daya daga cikin wadanda suka yi wannan aiki a lokacin zabe suna yi wa Allah Godiya kima suna godewa Darakta Janar da hukumar da ke kula da ingantuwar ayyuka Dokta Baffa Babba Dan Agundi godiya da kokarin da ya yi na daukaka kingiyoyin nan saboda wannan shi ne karo na biyu kenan da aka samu gudunmawa irin wannan domin ko a can baya sai da Uba Sani ya tara kungiyoyi guda dari hudu 400 ya kuma ba kowa Naira dubu dari kuma ga shi a yanzu ma wannan na shirin ba kungiyoyi sama da 347 tallafin da kowa zai samu ya taimaki kansa
Bawa sai ya yi kira ga yan kungiyoyi da su rike gaskiya da amana tare ci gaba da yin aiki tukuru su sani cewa ya dace a kara kaimin yi wa jam’iyyar APC aiki a shekarar 2027 a sake zaben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Sanata Uba Sani matsayin Gwamnan jihar Kaduna karo na biyu sannan a zabi dukkan yan takarar jam’iyyar APC a dukkan kukeru.
Sai Bawa FCNA ya ci gaba da yin bayanin abin da yake nufi da hadin kai saboda ko shi Darakta Janar na hukumar ingantuwar ayyuka Dokta Baffa Babba Dan Agundi ya ce baya son a rika yin tafiya a ware ya na son ayi aiki tare ne kawai a koda yaushe kuma ya nada yan asalin jihar Kaduna mukamai sannan kuma ga mai bayar da shawara a gare shi da yake aiki a nan Kaduna a cikin ikon Allah sai ga abin komai ya kankama sosai jama’a da dama duk sun hallara.

Don haka mu a Jihar Kaduna muna yi wa Dokta Baffa Babba Dan Agundi godiya domin a katon farko mun je mun kuma ga shugaban jam’iyya na kasa Dokta Abdullahi Umar Ganduje, mun ga James Falake da ministar Kwadago dukkansu ido da ido muka gansu wanda in ba domin hakan ba ta dalilinsa ba ba za mu ta ba samun wannan damar ba mu a mataayin kungiyoyi mu gansu su ganmu hakika wannan abin a ya ba ne kwarai.
Da take tofa albarkacin bakinta Barista Hasana Enok Kiyaru, babbar mai bayar da shawara ga shugaban hukumar kula da ingantuwar ayyuka ta kasa Dokta Baffa Babba Dan Agindi a kan gamayyar kungiyoyi na jihar Kaduna kira ta yi ga gammayar kunhiyoyin da su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga datakta janar baffa babba Dan Agundi domin inganta tafiyar da ake ciki.

Sai Barista Hassana ta yi kira ga daukacin mata baki daya da su bayar da goyon bayan da darakta Janar na hukumar ingantuwar ayyuka ke bukata.
Ita ma da take tofa albarkacin bakinta Hajiya Hauwa Muhammed daga jihar Kaduna a karamar hukumar Kaduna ta Kudu kuma ita ce mai huldar sadarwa tsakanin kingiyoyin gamayyar da ke karkashin APC daga ofishin Dokta Baffa Babba Dan Agundi, hakika wannan al’amari ya yi kyau kwarai domin yadda lamarin yake ana tunawa ne da mutanen da suka taimakawa tafiyar APC a zabubbukan Gwamna Uba Sani da Bola Tinubu wadanda suka taimaka ne z a fara yi wa tallafi ba wadanda za su zo a yau yau ba domin a dafa a ci gaba da tafiya.

Sai ta bayar da tabbaci ga sauran kungiyoyi da cewa duk ba za a mance da su ba domin a yanzu za a koma a kansu a san tafiyar kowa har a rankaya baki daya za a hada kai domin samun nasara