Home / Uncategorized / Muna Kira Ga Hon. Muttaka Rini Makaman Zamfara Ya Fito Takara – Kwamared Namanga Shinkafi

Muna Kira Ga Hon. Muttaka Rini Makaman Zamfara Ya Fito Takara – Kwamared Namanga Shinkafi

Daga Imrana Abdullahi
Wadansu zunzurutun matasa masu jini a jika daga Jihar Zamfara da suka kai sama da miliyan daya karkashin jagorancin Kwamared Namanga Muhammad Shinkafi suna yin kira ga daukacin al’umma baki daya a kowane language da sako na jihar da su goya masu baya domin tilastawa Honarabul Muttaka Rini makaman Zamfara da ya yi wa Allah ya fito takarar Gwamnan Jihar Zamfara domin ceto al’ummar jihar arewacin Najeriya da kasa baki daya daga cikin halin da suke ciki na rashin tsaro da tsananin rayuwa.
Shugaban Kwamitin fadakarwa da wayar da kan jama’a a game da wannan tafiyar Kwamared Namanga Muhammad ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake ganawa da manema labarai.
Kwamared Namanga Muhammad ya ci gaba da bayanin cewa sun yi wannan gangamin hada kar kungiyoyi ne na masu zaman kansu bisa la’akari da irin nagarta da kokarin Makaman Zamfara Honarabul Muttaka Rini, wanda a siyasance da sauran al’amuran da suka shafi hidimar siyasa tare da jagoranci kowa na yabawa da irin nagarta da yadda yake tafiyar da al’umma
 Saboda haka ne muka ga lallai ya dace sai mun yi duk mai yiwuwa domin fadakar da jama’a su shigo domin wannan bawan Allah mai hakuri da son jama’a ya amince ya taho domin yin takararar gwamnan jihar Zamfara.
Idan aka yi duba sosai da idanun basira za a ga cewa ko a lokacin da Honarabul Muttaka Rini Makaman Zamfara ya zama Dan majalisar wakilai ta kasa ya zama wakili guda daya tilo daga Jihar Zamfara da ya kasance a majalisar Abuja da babu kamarsa domin a koda yaushe duniya ta shaida irin yadda ya kasance a doron majalisa ya na tashi ya gabatar da jawabai da muhimman kudirorin kare martabat jama’ar mazabarsa, jihar Zamfara da na kasa baki daya, ya kan gabatar, goyon baya da kuma shiga a gaban majalisa a tatyauna duk wani judirin da aka gabatarwa majalisa wanda kuma daman shi ne aikin Dan majalisa
A waje daya kuma kowa zai uya shaidawa irin yadda yake kishi da dabbaka ayyukan ci gaban addinin Islama wanda a koda yaushe baya kasa a gwiwa wajen zuwa da kansa da kuma bayar da gagarumar gudunmawa wajen ganin addinin Allah ya kara daukaka.
Bugu da kari kuma Honarabul Muttaka Rini mutum ne da ke da kyakkyawar dangantaka da alaka mai kyau da manya da kananan a cikin al’umma, a takaice dai mutum ne da ke ganin girman kowa wanda hakan ta sanya manyan jihar Zamfara da kasa baki daya suke jiniina masa da kuma son yin alaka ta al’amuran yau da kullum da shi kuma kwalliya na biyan kudin sabulu kasancewar Honarabul Muttaka Rini Makaman Zamfara mutum ne mai amana da son aikata gaskiya da rikon ta a koda yaushe.
“A saboda haka ne mu zunzurutun matasa masu jini a jika da muka kai sama da miliyan daya daga jihar Zamfara muke cewa wannan nagartaccen shugaba da ya kasance a halin yanzu shugaban hukumar Kidayar jama’a mai kula da Jihar Zamfara baki daya Honarabul Muttaka Rini da ya yi wa Allah da Annabinsa, Annabi Muhammadu S.A .W da ya karbi kiraye kirayen mu ya share mana hawaye ya tsaya takara domin ceton al’umma baki daya domin shi duk abin da yake yi ya na tafiya tare da rungumar kowa nasa ne baki daya”, Inji Kwamared Namanga Muhammad.

About andiya

Check Also

10,000 South East Pupils Get School Bags From Collins Onyeaji Foundation

    No fewer than 10,000 pupils in the South East Zone of Nigeria are …

Leave a Reply

Your email address will not be published.