A Ranar Labaraba 4 ga watan Yuni 2025, Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Funtua da Dandume, Barista Abubakar Muhammad Gardi, ya kaddamar da sabbin azuzuwan karatu da aka gina a makarantu daban-daban a mazabarsa domin bunkasa ilimi da inganta yanayin karatu ga dalibai.
A karamar hukumar Funtua, an bude gìnin guda biyu ne masu ajujuwa shida a unguwar Mai Gamji, inda Dan majalisar ya bayyana cewa gine-ginen za su taimaka matuka wajen rage cinkoso a ajujuwa da kuma kara ingancin koyarwa da koyo.
Haka zalika, a karamar hukumar Dandume, an kaddamar da block biyu na azuzuwa shida a makarantar Sakandaren al’umma Kwaminiti da ke cikin gundumar Dandume. Sauran ajujuwan da aka bude sun hada da wasu biyu da aka gina a makarantar Firamare ta Dajin Mare domin kara fadada damar ilimi ga yara masu tasowa a yankin.

Abubakar Gardi ya ce wannan aiki yana daga cikin tsare-tsaren da ya kuduri aniyar aiwatarwa don inganta rayuwar al’ummar mazabarsa ta hanyar samar da muhalli mai inganci na ilimi.
A jawabin da ya gabatar yayin bikin kaddamarwar, Honarabul Abubakar Muhammad ya ce “Kullum burina shi ne in ga yara na zuwa makaranta da kwarin gwiwa tare da mayar da hankali wajen karatu. Ina kira gare ku ku ci gaba da jajircewa domin cimma nasara.

Manyan baki da dama ne suka halarci taron, da suka hada da Darakta Janar (D G) Alhaji Rabiu Kanar, da shugaban kungiyar malaman firamare ta kasa (NUT) reshen Dandume, Malam Shamsuddeen Sani.
Sauran wadanda suka halarta sun hada da shugabannin kananan hukumomin Funtua da Dandume, wakilai daga ofishin kwamishinan lafiya na jihar Katsina, da kuma wakilan hakiman yankunan Funtua da Dandume.
THESHIELD Garkuwa