Home / Labarai / Gwamnatin Kaduna Ta Sanya Dokar Hana Fita Awa 24 A Gundumar Atyap Da Chawai

Gwamnatin Kaduna Ta Sanya Dokar Hana Fita Awa 24 A Gundumar Atyap Da Chawai

 Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana Sanya dokar hana fita tsawon Awa 24 a gundumar Atyap da ke karamar hukumar Zangon Kataf da kuma Chawai a karamar hukumar Kauru.
Wannan dokar hana fita ta awa 24 ta fara aiki ne nan nake.
 Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun kwamishinan kula da harkokin tsaron cikin gida da al’amuran cikin Gida Samuel Aruwan.
Jami’an tsaro suna kokarin tabbatar da zaman lafiya daga irin yadda al’amura suke ciki biyo bayan yadda aka samu tashin tashina a satin da ya gabata saboda rikicin fili a Zangon Kataf da shugabannin jama’a suka yi kokarin kwantarwa amma kuma lamarin ya yadu.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.