Sakamakon irin kiraye kirayen da Ake yi a kan zancen komawa jam’iyyar APC na Mai girma Garkuwan Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya sa “ban amince ba, saboda nayi magana dashi kai tsaye ya tabbatar man da matsayarsa ta ya aje batun jam’iyya ko shiga hayaniyar siyasa kowace iri a yanzu.
Labari ne na rashin fahimta, wasu daga cikin magoya bayansa ne suka yiwa kansu mafita akan baiyana ra’ayinsu da suke son goyon baya daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Mai girma Garkuwan Sokoto, Attahiru Bafarawa bai shiga kowace jam’iyyar siyasa ba a yanzu; wannan haka take a ra’ayinsa, yana nan uba ga kowane dan jam’iyya a jahar Sokoto dake neman shawararsa.
Zai fitar da Sanarwa da kansa dangane da wannan hayaniya a nan gaba.
Mun dai samu wannan sanarwa ne daga Yusuf Dingyadi
THESHIELD Garkuwa