Daga Imrana Abdullahi
Sakamakon irin yadda al’amuran siyasa suka hargitse a jihar Kano tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma mai gidansa Injiniya Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso, ya Mustapha Rabi’u Kwankwaso wanda shi ne Kwamishinan ma’aikatar kula da harkokin wasanni da matasa a Jihar Kano ya ajiye aikinsa.
Kuma ya fice a matsayin memba a majalisar zartas War Jihar Kano
Hakika ina sanar da cewa a matsayina na Kwamishinan ma’aikatar kula da harkokin wasanni da al’amuran ci gaban matasa na jihar Kano na ajiye wannan aikin.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun Mustapha Rabi’u Kwankwaso a matsayin tsohon Kwamishina.
Mustapha Kwankwaso ya ci gaba da bayanin cewa a cikin takardar ta sa ya na matukar godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya bashi ya yi aikin Kwamishina wanda hakan ya bashi damar yi wa jama’ar Jihar Kano hidima. Hakika na samu wata kwarewar da a can baya ba Ni da ita.
Na ajiye aiki, ina kuma yin addu’ar Allah ya sa matasan Jihar Kano za su ci gaba da samun kulawar da ya dace.
Ina kuma yin addu’ar Allah ya ci gaba da taimakawa Jihar Kano.ina kuma yi wa jama’ar Jihar Kano fatan alkairi.
Mustapha Rabi’u Kwankwaso
Tsohon Kwamishinan ma’aikatar Matasa da ci gaban Wasanni
THESHIELD Garkuwa