Related Articles
Imrana Abdullahi
Hukumar da ke kula da ababen hawa ta Jihar Kano KAROTA ta bayyana cewa ta kai kamfanonin motocin sufuri gaban kuliya ne saboda kunnen kashin da suka nuna game da umarnin hukumar.
Shugaban hukumar KAROTA na Jihar Kano Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana hakan inda ya ce kamfanonin manyan motocin sufurin sun kasa aiwatar da bin tsarin da Gwamnatin ta shimfida masu tun farko.
“Mun nunawa wadannan motocin sufuri wurin da za su koma domin Gwamnati na son kiyaye doka da oda tare da tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar jama’a”.
Ya ci gaba da cewa muna son tattara wadannan kamfanoni wuri daya ne domin tabbatar da tsaro ba kawai kowa ya rika aiwatar da abin da yaga dama ba
“Tun da suka yi kunnen kashi da tsarin da Gwamnatin ta fitar da kowane ya koma can inda Gwamnatin ta samar masu shi yasa muka je kotun domin ita da kanta kotun ta gaya masu me ake ciki kuma kowa ya san matsayisa”.
Baffa, ya ce ta irin wannan hanya ne ake shigo mana da wadansu abubuwan da ba su dace ba kamar kwayoyi, makamai da sauran haramtattun abubuwa, don haka Gwamnati ba za ta yi kasa a Gwiwa ba sam.
A ta bakin wadansu masu kamfanonin dai sun bayyana cewa tuni su sun biya kudin harajin da ya dace su biya to, amma ba su san ko akwai wadanda ba su biya ba.
Amma dai zamu zauna da Gwamnati muga me ya dace ta hanyar tattaunawa.