Home / Labarai / Safarar Mutane: Hukumar NAPTIP Ta Ceto Mutane 132 A Akwa Ibom

Safarar Mutane: Hukumar NAPTIP Ta Ceto Mutane 132 A Akwa Ibom

 Imrana Abdullahi
Hukumar da ke yaki da safarar bil’adama ta kasa NAPTIP, shiyyar Uyo, ta bayyana cewa sun samu nasarar ceto mutane 132 a cikin watanni Takwas.

Darakta Janar na hukumar, Dame Julie Okah- Donli be ya bayyana hakan lokacin da take ganawa da manema labarai a lokacin da ta kai ziyara Jihar a ranar Alhamis da ta gabata.

Okay Donli daga cikin mutanen 40 an tseratar da su ne daga matsalar yin lalata, mutane 28 kuma daga masu sana’ar sayar da jarirai, 23 kuma daga masu Sanya kananan yara aikin karfi, sai ta kara da cewa kashi 40 daga cikinsu sun fito ne daga karamar hukumar Oron a Jihar.

Ta ce ” wadanda aka tseratar shekarunsu sun kama daga biyar (5) zuwa 34.Kuma Kawhi 40 sun fito ne daga karamar hukumar Oron ne saboda kusancin wurin kogin Atalantika”.

Daraktar ta shaidawa manema labarai cewa ta zo ne domin kaddamar da kwamitin karta kwana a kan yaki da safarar mutane kuma bayan hakan nan za ta gana da masu ruwa da tsaki da suka hada da sarakuna, kungiyoyi masu zaman kansu da makamantansu duk a kokarin yin yaki da batun safarar bil’adama a kasa baki daya.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.