Home / Ilimi / Za A Kafa Harsashin Ginin Jami’ar Karaduwa – Nura Khalil

Za A Kafa Harsashin Ginin Jami’ar Karaduwa – Nura Khalil

Za A Kafa Harsashin Ginin Jami’ar Karaduwa – Nura Khalil
Mustapha Imrana Abdullahi
Wani mai kishin al’ummar Jihar Katsina da arewacin N8jeriya baki daya kuma shahararren dan siyasa da ya yi takarar neman kujerar Gwamnan Jihar Katsina ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba za a kafa harsashin ginin jami’ar Karaduwa mai zaman kanta
Injiniya Nura Khalil, ya ce “Ina mai matukar farin cikin shaida ma al’umma cewa, nan da ‘yan kwanaki kadan, cikin yardar Allah, zamu kafa harsashin fara ginin Jami’ar Karadua, watau, University of Karadua, a filin ta na dundundin”.
Ayyukan da za’a fara a wannan fili, sun hada da katangar haraba, ofishin hukumar Jami’a, azuzuwa, dakunan hade hade da bincike na fagen kimiyya da fasaha, asibiti, dakunan kwana, dakunan cin abinci, masallatai, da kuma ofisoshin tsaro dana ‘yan kwana kwana.
Wannan yunkuri, yana cikin kammala  bukatun hukumar kula da jami’o’i ta kasa domin bada iznin kafuwa da kuma fara karatu ga Jami’ar.
Da wannan yunkuri za a iya cewa wannan bawan Allah Injiniya Nura Khalili, ya kafa turbar sharewa jama’a hawaye kenan saboda da man rashin babbar makaranta na daya daga cikin irin matsalar da ke Damuwar mutanen wannan yanki nanKudancin Katsina da ake kira da yankin Karaduwa.
Fata dai shi ne Allah ya yasa a fara a sa’a tare samun duk wata nasarar davaka bukatar samu.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.