Related Articles
Babu Dan Siyasa Irin Balarabe Musa – Sama’ila Suleiman
Imrana Abdullahi
Dan majalisar Wakilai ta tarayya mai wakiltar karamar hukumar Kaduna ta Arewa honarabul Sama’ila Suleiman ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.
Sama’ila Suleiman ya ce hakika daya da daya idan za a tantance irin yadda batun rikon gaskiya da Amana s hadimar yau da kullum ko a fagen siyasa babu kamar marigayi Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa.
Honarabul ya tabbatarwa manema labarai cewa ” ko shugaba Buhari bai kai marigayi Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ba a wajen rikon Amana, saukin kai da kuma zama tare da jama’a musamman Talakawa na kasa”.
Ya ce ” a matsayinsa na tsohon Gwamna kuma jagoran jam’iyyar PRP a kasa baki daya, amma shi ne ke zama wakilin Jam’iyyarsa a akwatin zabe ya kare Jam’iyyarsa mu kuma a matsayinmu na kananan yara my kare akwatin zaben a bangaren kuri’armu a inda aka ajiye akwatin zabe a makarantar horar da ma’aikatan Gwamnatin tarayya da ke Unguwar Malali Kaduna, hakika wannan babu wani Gwamna da zai iya hakan”.
“Kai magana ta gaskiya Balarabe Musa ya fi Buhari inganci a batun shugabanci da kuma kokarin tafiya da na can kasa duk Nijeriya babu kamar Balarabe Musa, dan majalisa Sama’ila Suleiman yana magana da yan jarida yana kuka saboda alhinin rashin da aka yi”.
Ya ce ba zai mance da wani abu da ya gani ba a wata rana ” ina kan hanya wajen Kawo sai Naga motarsa ta lalace a kusa da babban Barikin soja a runduna ta daya ya tsaya motarsa ta lalace nan muka tsaya muka bayar da mota aka kawo shi gida kuma motarsa aka gyara ta, hakika ba za a samu Gwamnan da zai kasance a hakan ba sai Balarabe Musa saboda gaskiyarsa da rikon amana”.