Home / Labarai / Gwamna Zulum Ya Rabawa Jama’a Miliyan 80, Kayan Abinci Ga Mata Dubu 16 Yan Gudunhijira

Gwamna Zulum Ya Rabawa Jama’a Miliyan 80, Kayan Abinci Ga Mata Dubu 16 Yan Gudunhijira

Gwamna Zulum Ya Rabawa Jama’a Miliyan 80, Kayan Abinci Ga Mata Dubu 16 Yan Gudunhijira
Mustapha Imrana Abdullahi
Bayan kammala rabon makudan kudi tare da kayan abinci ga matan da suka dawo garin Gwoza daga gudun hijira, nan take Gwamnan ya kuma bayar da umarnin a sake gina gidajen malaman Makaranta 33 domin ci gaba da karatu.
Hakazalika Gwamna Zulum ya kuma sanar da yin hanin bangar siyasa ga dukkan daukacin Jihar baki daya.
Gwamna Babagana Umara Zulum a yanar Lahadin da ta gabata ne ya ziyarci wurin inda ake rabon kudi naira miliyan 80 da kuma kayan abinci ga mata dubu 16 da suka dawo daga gudunhijira zuwa cikin garin Gwoza a matsayin abin da Gwamnan Gwamnan aiwatar a rana ta biyu domin aikin jikan jama’a a garin Gwoza da kuma kauyukan yankin Borno ta Kudi.
Gwamnan wanda ya Isa garin Gwoza a ranar Juma’a, sai a ranar Asabar da ya duba aikin rabon kudi miliyan 150 ha matsakaita da kananan masana’antu da kuma kayan abinci ga mutane dubu 27, da sula hada maza da suka zo bayan gujewa matsalar Boko Haram.
A ranar Lahadi ya ci gaba da aikin raba kudi ga mata dubu 16 inda kowace ta samu naira dubu biyar domin su samu taimakawa kansu da irin abincin da aka ba su.
Taimakon wani bangare ne na ci gaba da taimakawa al’ummar da harkokin neman abincinsu suka samu  matsala sakamakon matsalar yan Boko Haram.
Garin Gwoza Gwoza samu matsalar kasancewa a karkashin Yan Boko Haram daga shekarar 2014 zuwa 2015 inda wani faifan bidiyon da ke nuna Abubakar Shekau yana amfani da garin Gwoza a matsayin hedikwatar da suke aiwatar da ayyukansu na Boko Haram. Amma dai jami’an tsaron Soja suka kwato garin a shekarar 2015.
Yan Boko Haram din lokacin da suka zauna garin sun bata daruruwan gidajejama’a  da kuma kayan Gwamnati da aka yi domin amfanin jama’a musamman gidaje
A kokarin ganin harkar ilimi ta dawo a baki dayan kananan hukumomin Jihar, Zulum ya yi amfani da zuwansa Gwoza inda ya tattauna da malaman makarantar sakandaren Gwamnati  da kuma na makarantar sakandaren jeka ka dawo duk a garin Gwoza.
Ya dai bayar da umarnin yin aiki mai inganci na gidajen malaman makaranta 33 da yan Boko Haram suka lalata a shekarar 2014 da ta gabata.
Banda ginin gidajen malaman makaranta Gwamna Zulum ya kuma bayar da umarnin kara daukar malaman makaranta guda shida domin raba su ga makarantu biyu da ya tattauna da su wanda suka bukaci hakan.
Gwamna Babagana Umara Zulum a ranar Lahadi a Gwoza ya bayyana batun karin lokacin hani kan batun bangar siyasa ga daukacin kananan hukumomin Jihar Borno 27  baki daya.
A cikin watan Yuli na shekarar 2019 Gwamna Zulum ya bayar da umarnin yin hani ga dukkan ayyukan bangar siyasa a Maiduguru da kuma karamar hukumar Biu Biu watan Janairu 2021. Kuma a ranar Asabar, Gwamnan ya yi hani game da bangar siyasa a garin Gwoza inda Gwamnan ya kwashe tsawon kwanaki biyu ya na ziyarar aiki.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.