Home / Labarai / Gwamnatin Kaduna Ta Dakatar Da Kasuwannin Birnin Gwari,Chikun,Giwa,Igabi Da Kajuru Masu Ci Sati Sati

Gwamnatin Kaduna Ta Dakatar Da Kasuwannin Birnin Gwari,Chikun,Giwa,Igabi Da Kajuru Masu Ci Sati Sati

Mustapha Imrana Abdullahi
…An hana sayar da Fetur a cikin jarkoki a kananan hukumomin Birnin Gwari,Chikun,Giwa,Igabi Da Kajuru.
Bayan yin duba sosai a game da harkokin matsalolin tsaro hukumomin tsaro sun fitar da wadannan matakai, bisa duba da wannan yanayi Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da Dakatar da dukkan wadannan kasuwanni masu ci a sati sati a kananan hukumomin Birnin Gwari,Igabi, Giwa, Chikun da Kajuru nan take.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da ke dauke da sa hannun Kwamishinan ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida Malam Samuel Aruwan.
Gwamnatin ta kuma hana sayar da man fetur a cikin jarkoki a ciki da wajen gidajen mai a wadannan kananan hukumomi gida biyar da aka lissafa shi ma nan take.
An kuma bayar da umarni ga jami’an tsaro da su tabbatar da kowa ya bi wannan dokar.
Gwamnatin kuma ta umarni daukacin jama’a da su ci gaba da bayar da hadin kai da goyon baya ga wannan matakan da aka dauka domin magance matsalar yan bindiga da ayyukan batagari da suke yin barazana ga harkokin tsaro a cikin Jihar.
An kuma umartar jama’a da za su bayar da muhimman bayanai da su yi amfani da wadannan layukan waya.
09034000060
08170189999

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.