Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
Kamar yadda jaridar daily trust ta ruwaito a yau Alhamis shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa ya yanke jiki ya fadi a fadar shugaban kasa a lokacin da ya ke jawabi a wurin taron ranar Sanin kai,wato National Identity Day.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa Bawa ya fara jawabin sa kenan bai dade ba sai kawai ya fara rufe fuska da hannu yan cewa ayi hakuri ba zan iya magana ba, a zo a taimake ni, daga nan ne ministan sadarwa ya rike shi zuwa wurin zama. Sai dai kuma ko da ya zauna sai ya kasa zama ya yanke jiki ya fadi.
Daga nan sai aka taimaka masa aka fita dashi daga dakin taron.