Home / Labarai / Ga Takaitaccen Tarihin Sabon Sarkin Kano

Ga Takaitaccen Tarihin Sabon Sarkin Kano

Daga Imrana Abdullahi
An haifi sabon Sarkin Kano Kano shekarar 1963 a garin Kano, ya fara karatun boko a makarantar gidan Makama da ke kusa da gidan ajiye Tarihi na Gidan Makama a birnin Kano.
Bayan nan ya shiga makarantar sakandare ta Gwale. Sai kuma karatun digirinsa na farko a jami’ar Bayero da ke Kano inda ya yi karatun koyon aikin jarida, ya yi aikin yi wa kasa hidima a gidan Talbijin na NTA da ke Makurdi, a Jihar Banuwai.
 Sabon Sarkin na Kano ya kuma rike sarautu daban daban a tsawon shekaru Talatin, a shekarar 1990, an Dana shi sarautar Danmajen Kano, daga baya aka nada shi sarautar Danburan Kano, Sai kuma Turakin Kano sai Sarkin Dawakin tsakar gida daga nan Wamban Kano kafin ya zama Sarkin masarautar Bichi.

About andiya

Check Also

Backward Integration: Dangote Targets 700,000MT of Refined Sugar in Four years

    …As Q1 revenue rise by 20.1% to N122.7bn   Dangote Sugar Refinery Plc …

Leave a Reply

Your email address will not be published.