Related Articles
Daga IMRANA ABDULLAHI, Kaduna
Dimbin jiga Jigan yan Najeriya ne suka rika yin tururuwa a Jihar Kaduna domin yin gaisuwar ta’aziyya ga iyalan marigayi Bukar Shettima, tsohon babban jami’in yan Sanda da ya rasu ya na da shekaru 94 a duniya.
Daga cikin manyan mutane daga Najeriya da suka gai wa iyalan marigayin gaisuwar ta’aziyya akwai Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El- Rufa’I, tsohon mataimakin shugaban kasa Muhammadu Namadi Sambo, Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello, Alhaji Aliko Dangote, Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na biyu, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Ahmed Muhammad Makarfi da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Muktar Ramalan Yero da tsohon Gwamnan Jihar Adamawa Alhaji Jibirila Bindo.
Sauran sun hada da shugaban kamfanin Matrix Energy Abdulkadir Aliu, ACG a rundunar kwastan Alhaji Sani Nuhu, Sanata Uba Sani, Honarabul Isa Ashiru Kudan da Alhaji Adamu Attah.
Daga cikin muhimman mutanen da suka halarci gidan marigayin sun hada da mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Hadiza Sabuwa Balarabe da dai sauransu da dama.
Marigayi Shettima ya zamo daga cikin yan kasa na farko da suka shiga aikin dan Sanda da ya yi aiki a rundunar Yan Sandan Jihar Kano da Kaduna.
Ya dai ajiye aiki ne a matsayin kwamishinan Yan Sanda da kuma Daraktan rundunar tsaron yan sandan ciki na kasa (NSO). Bayan ya ajiye aiki an kira shi ya zama shugaban kananan hukumomin Magumeri da Kaga a Jihar Borno.
Da yake tattaunawa da manema labarai a ranar satin da ya gabata, daya daga cikin yayan bayyana marigayin ya yi da cewa mutum ne mai kokarin tabbatar da da’a da biyayya kuma mai kokarin kwamar cin hanci da rashawa.
Alhaji Ibrahim ABBA Gubio kuma wanda ya kasance tsohon jami’in tsaro mai murabus cewa ya yi hakika marigayin abin ko yi ne da za a rasa shi da kuma halayensa abin yin koyi wadanda ya taimaka wa kasa da su aka samu gagarumin ci gaba.
Da shima yaka gabatar da nasa jawabin wani shugaban al’umma dan uwa ga marigayi Shettima, Bulama Mali Gubio (mni) ya bayyana marigayin da cewa mutumin kirki ne da ke yaki da halaye marasa kyau kuma ga shi mutum mai sa’a da biyayya da ke da karfin Gwiwar tsaya wa kan gaskiya da tabbatar da adalci.
Marigayi Alhaji Bukar Shetima ya rasu ne watan Azumin da aka kammala kwanan nan, ya kuma rasu ya bar Yaya sha hudu 14, da jikoki da dama daga cikinsu akwai Alhaji Kashim Bukar Shetima shugaban kamfanin Barbedos Guruf da Hajiya Maryam Bayi, tsohuwar Darakta a hukumar kula da harkokin sadarwa ta kasa.