Daga Imrana Abdullahi
Mai Alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga daukacin al’ummar musulmi a tarayyar Najeriya da su fara duban jinjirin watan Shawwal na shekarar musulunci ta 1446 a ranar Asabar mai zuwa da ta yi dai dai da ranar 29 ga watan Maris 2025.