Home / Labarai / An Binne Wata Budurwa Da Ranta A Kafur

An Binne Wata Budurwa Da Ranta A Kafur

Daga Wakilin mu
Bisa kuskuren da ya faru a wani gari da ke Kafur cikin karamar hukumar Kafur a Jihar Katsina, rahotanni sun bayyana cewa an yi kuskuren binne wata budurwar da ake tsammanin ta mutu.
Sa’adatu Hassan Kafur, ta samu matsalar ta ba wutar lantarki ne wanda sakamakon hakan aka dauki Sa’adatu zuwa asibiti cikin gaggawa domin a tabbatar da halin da ake ciki.
Rahotannin sun bayyana cewa duk da an Kaita asibitin domin duba lafiyar Sa’adatu, amma duk da hakan wani a asibitin ya ce ta rasu.
Sakamakon hakan ne wadansu mutane suka yi kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da ta hanzarta aiwatar da ingantaccen bincike game da halin da asibitoci da masu aiki a asibitin suke ciki domin tantancesu bisa doka ta yadda za a samu ingantawar aikin lafiyar jama’a baki daya.
Amma daga bayan an Kaita makabarta sai mutane suka rika yin rade radin cewa su na kokwanton rasuwar Sa’adatu domin sun ji a lokacin da suke dauke da ita cikin Makara kamar cikinta ya yi kuka, kuma sun ji ta yi Hutu amma gudun magana ya sa suka yi shuru da bakinsu.
Haka ma a bangaren wadanda suka kwana da ita a matsayin Gawa a cikin daki sun ji motsi a cikin makarar da aka Sanya ta a ciki, amma sai suka yi tsammani Bera ne ya gitta cikin makarar, kasancewar daman an yi mata wanka an hada ta kamar yadda addinin Islama ya tanadar, sabida kasancewar Dare ya yi sai aka ce sai gari ya waye tukuna a Kaita.
Nan da nana aka dunguma zuwa makabarta aka kuma tone ramin da take ciki aka fito da ita da ranta, sai aka ta fi da ita asibitin garin Malumfashi inda kafin a samu damar aikin sai ta ce ga garinku nan, wato dai a yanzu ta Riga mu gidan Gaskiya.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.