Fadar mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Dokta Sa’ad Abubakar ta sanar da ganin jinjirin watan Ramadan da maraicen ranar Juma’a.
Cikin wata sanarwa da Sarkin Musulmin, Sa’ad Abubakar lll ya karanta a fadarsa, ya ce an ga watan a sassan ƙasar daban-daban.
Don haka ne ya ayyana ranar Asabar 1 ga watan Maris a matsayin 1 ga watan Ramadan 1446.
Tuni dai hukumomin Saudiyya suka sanar da ganin watan a ƙasar, inda suka ayyana gobe Asabar a matsayin ɗaya ga watan Ramadan a Saudiyya.