Home / Uncategorized / An Jinjina Wa Dogarin Shugaban Kasa DCP Usman Shugaba Da Sama Wa Matasa 50 Aikin Yan Sanda

An Jinjina Wa Dogarin Shugaban Kasa DCP Usman Shugaba Da Sama Wa Matasa 50 Aikin Yan Sanda

….Mun Shirya Liyafa Ne Domin   Murnar Daukar Matasa 50 Aikin Dan Sanda
Daga Imrana Abdullahi
Abubakar ..ya bayyana cewa sun hada taron liyafa ne domin murnar daukar matasa 50 aikin Yan Sanda da dogarin shugaban kasa DCP Usman Musa Shugaba ya yi a Jihar Kaduna.
Abubakar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai, inda ya ce an yi wannan ne domin kokarin da wannan bawan Allah mai kishin al’umma ya yi dogarin shugaban kasa DCP Usman Shugaba na samawa yara matasa 50 aikin Yan Sanda a cikin garin Kaduna domin hakika lamari ne na a ya ba kasancewar ba a ta ba samun wani abu mai kamar hakan ba a cikin tarihi.
“Hakika muna yin murna da wannan kokarin kuma muna yin kira ga wadannan yara da su zama jagorori nagari a bayan kasa su kuma zama masu bin doka da oda saboda a yanzu duk abin da suka yi ana kallonsu ne a matsayin mutanen mai girma shugaba ne da ya sama masu wannan aikin da kuma hukumar yan Sanda ta Najeriya kasancewar su jami’anta ne don haka ne muke rokonsu da su zama yan Sanda nagari kada su aikata duk wani abu da ya sabawa dokar kasa.
Da yake tofa albarkacin bakinsa wakilin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alh. Shittu Ibrahim Dikko Dangaladiman Wazirin Zazzau Shitu Ibrahim, godiya ya yi wa Allah madaukakin Sarki da ya ba al’umma irin wannan mutum Usman Shugaba
Sai ya bayar da shawara ga wadanda suka samu nasarar zama jami’an Yan Sanda ta sanadiyyar kokarin Usman Shugaba da cewa ya dace su zama masu gaskiya da rikon Amana a koda yaushe wajen gudanar da ayyukansu na tsare doka da oda a cikin al’umma su kuma rika yin aiki kai tsaye ba tare da karbar duk wani abu da ba na su ba ne.
“Su kasance duk abin da za su karba ya zama abu ne da doka ta amince da hakan kuma duk abin da doka ba ta ba su damar hakan ba su guje shi kwata kwata, su kuma guji yin shaye shaye ko duk abin da zai kawar masu da hankali”.
Alhaji Shitu ya kuma ce ya na ba su shawara da cewa a duk inda aka aika su domin yin aiki lallai su zama wakilai nagari masu rikon gaskiya da aiki tukuru ba tare da gajiyawa ba saboda aikin dan Sanda ba aiki ba ne da mutum zai yi shi kamar yadda ya ga dama don haka dole ne su kasance da tarbiyya da yin Da’a kamar yadda aka horar da su a lokacin da suke kwalejin bayar da horon aiki.
Mugu da kari kuma ya dace su Sani cewa wannan ne fa matakinsu na farko wato dai a yanzu suka fara don haka su yi duk abin da ya dace su samu ilimi a bangarori daban daban ta yadda zai taimakesu wajen aiwatar da aikin
Muna fatan Allah ya taimaka masu ya yi masu jagora.

About andiya

Check Also

Dangote sets to buy 12m barrels of crude oil from United States for refinery operations

  The Dangote Petroleum Refinery is awaiting up to 12 million barrels of crude oil …

Leave a Reply

Your email address will not be published.