Mustapha Imrana Abdullahi
Sakamakon irin halin da shugaban Jami’an tsaron sa kai na Civilian JTF Aminu Sani ya samu kansa a ciki wanda a lokacin rubuta wannan rahoton ke kwance a kan Gadon asibitin kwararrun na sojoji ya na neman daukin kulawar gaggawa.
Kamar yadda lauyansa mai suna Aminu Abdurasheed ya shaidawa manema labarai a garin Kaduna cewa halin da mutumin da yake tsayawa ke ciki wato Aminu Sani a gaskiya hali ne na bantakaici wanda ya dace duk wani mutum ko a ina yake ya tausaya masa.
“Mitum ne da ya shekara Bakwai ya na bayar da gudunmawarsa wajen taimakawa tsaron dukiya da lafiyar jama’a kamar yadda kowa ya Sani, musamman idan aka yi la’akari da irin yadda wadansu masu kwacen kayan jama’a suke fakewa a cikin jama’a su na aiwatar da mugun aikinsu, amma saboda irin yadda wadannan mutane masu aikin sa kai karkashin wannan mutum Aminu Sani ke aiwatar da ayyukansu ya taimakawa wajen samun zaman lafiya a tsakanin jama’a wanda hakan abin a ya ba ne kwarai”, inji Lauya Aminu.
Ya ci gaba da cewa duk da ba Albashi kowa ke biyansu ba amma sun sadaukar da rayuwarsu wajen ganin kowa ya zauna lafiya, ” ta yaya za a ce ayi wa wanda ke wannan kokari sakayya irin wannan?
“Ni a matsayin lauyansa na je asibitin na kuma same shi a can kwance kan gadon asibiti kwance cikin fitsarinsa sai wani dan Gajeren wando kawai, ba riga a jikinsa kuma daure cikin Ankwa da aka hada kararsa da gadon da yake kwance a kai, ya kuma shaida Mani cewa ya na bukatar a sama masa da Bargon rufa domin sanyin da yake ciki ya na damunsa har ya na ce Mani zai iya mutuwa saboda tsananin sanyi, na kuma lura cewa ya na tsananin bukatar abinci da ruwan sha tare da Karin ruwa a jikinsa domin tsananin dukan da ya sha ya galabaita shi har in banda kwanaki biyu nan bai ma san inda yake ba”, inji Lauya.
Lauya Aminu ya kara da cewa, ” Aminu Sani ya shaida masa cewa tun farko dai wani soja ne ya kira shi a waya da Daddare ya na son ganinsa bayan da ya ta fi ne suka rike shi a wurinsu suka kuma ta fi da shi can cikin Dajin wani kauyen da ake kira Maguzawa, kamar yadda Lauya ya shaidawa yan jarida cewa sai suka rika dukansa ba kakkautawa har bai san inda yake ba kuma da alama cewa kamar hannunsa wato Aminu Sani hannun hagun a karye yake sakamakon azabar da ya sha a wurinsu inda babu wani mataimaki sai Allah”.
Bisa irin wannan yanayi ne muka kai kara a gaban babbar kotun Jihar Kaduna domin neman adalci da kuma biyan Aminu Sani diyyar naira miliyan dari biyar sakamakon irin akuba, cin mutunci da tozarcin da aka yi masa wanda ya taka masa yanci a zamansa na dan kasa mai yanci.
Daga cikin wadanda aka kai karar sun hada da shugaban rundunar Sojan Najeriya, shugaban runduna ta daya (GOC) laftanar kanar Gada, wanda shi ne jagoran sojojin da ke unguwar hayin Rigasa kuma shi ne da kansa ya kira Aminu Sani cikin Dare amma kamar yadda Lauya Aminu, ya shaidawa manema cewa Aminu Sani ya gaya masa lokacin da ya je wurinsa a asibiti cewa sun azabtar da wanda yake tsayawa na tsawon kwanaki 15 da suka kai shi Dajin Maguzawa a Kaduna.
Lauya Aminu ya ce ” na rubuta takardar koke ga shugaban rundunar soja ta daya da ke Kaduna har zuwa ga rundunar sojan Najeriya amma babu wani bayanin da na ji daga wurinsu kuma na aika wani Lauya zuwa matsugunnin sojoji da ke Tashar Jirgin kasa cikin garin Kaduna nan ma ba wani labarin komai.
Har sai yau da na shigar da kara gaban babbar kotun Jihar Kaduna domin neman hakki kan abin da aka yi wa Aminu Sani shugaban jami’an Sa kai na Civilian JTF da ke Kaduna
Muna kuma fatan kotu za ta duba lamarin ta yi adalci a shari’ar tsakanin wanda aka taka wa hakki da kuma duk wanda ake kara, koda yake mun karanta a jarida cewa sojojin sun kama shi ne sakamakon bayanin da suka samu daga wani dan bindiga da suka kama cewa wai Aminu Sani na taimakon yan bindiga da bayanai, saboda hakan ne suka kama shi.
Lauya Aminu Abdurasheed ya ci gaba da cewa hakika babu wanda yake kin a hukunta duk wani mai laifi amma halin da Aminu Sani ke ciki an tauye masa hakki kwarai kuma hakan ya saba wa tanajin dokar kasa a kama mutum ya kai tsawon Awoyi 24 ba a gabatar da shi a gaban kotu ba.
Don haka ne muka rubuta takardar koke ga rundunar soja ta daya da ke Kaduna, kuma mun aika kofin takardar ga kwamishinan Yan Sanda na Jihar Kaduna, shugaban Yan Sanda farin kaya DSS da kuma shugaban rundunar yan Sanda ta kasa (IGP) mun kuma sanar da Gwamnatin Jihar Kaduna kasancewar Aminu Sani na daya daga cikin rundunar Yan sa kai da suke bayar da gudunmawarsu wajen samar da zaman lafiya da tsaro a koda yaushe.
“Muna yin kira ga daukacin jama’a baki daya da su zauna lafiya kowa ya ci gaba da gudanar da ayyukansa cikin kwanciyar hankali da lumana”.