Related Articles
Imrana Abdullahi
Sakamakon ruwan sama tare da Iska mai tsanani da aka yi a cikin garin Kaduna ya haifar da asara a gidaje inda rufin gidajen ya lalace, an kuma samu matsalar karyewar turakun wutar lantarki da katsewar wayoyin wutar lantarki.
Lamarin dai ya faru ne a unguwannin layin Sardauna kirestan, unguwar Oreya kwata da wani bangare na Tudun wada duk a cikin garin Kaduna.
Da wakilinmu ya zagaya a cikin garin kaduna domin ganewa idanunsa yadda matsalar ta faru, ya tarar da dimbin talakawan da lamarin ya shafa suna zaune a kofar gidajen da kwanukan rufin gidan suka tashi baki daya tare da rushewar Katangu da sauran gine gine.
Wadanda lamarin ya shafa sun yi ta kiraye kirayen Gwamnati da masu hannu da shuni da suzo domin taimaka masu saboda irin halin da suka shiga.