Home / Uncategorized / An Yi Taron Gangamin Wayar Da Kan Jama’a Illar Miyagun Kwayoyi A Yankin Arewa Maso Yamma

An Yi Taron Gangamin Wayar Da Kan Jama’a Illar Miyagun Kwayoyi A Yankin Arewa Maso Yamma

Dole Sai An dauki Kwakkwaran mataki game da batun ta’ammali da miyagin kwayoyi
A yankin arewa maso Yamma ana samun wanman illa kwarai ta masu yin ta’ammali da miyagun kwayoyi, musamman ma alkalumma daga jihar Kano na cewa kashi 40 na kata sun zunduma cikin wannan mataala, yayin da bisa abubuwan da suka faru a jihohi irin su Kadina, Katsina da Sakkwato na cewa ana samun karuwar hankar a shekara daya da ta gabata.
Sai dai a kananan hukumomi irinsu karamar hukumar Kano, Katsina ana samun taimakon yaki da wannan lamarin ta hanyar yin aikin hadin gwiwa da kungiyoyi masu zaman kansu da shugabannin al’umma wanda hakan ya sa ake samin cimma jama’ar da suka kasance masu karabiner karfi.
Shugabam majalisar wakilai ta kasa ya bayyana cewa zaben tattauna wannan lamarin na nufin irin yadda lamarin ke shafar harkokin tsaron dukiya da lafiyar jama’a.
Don haka lamarin ya wuce ya tsaya haka nan kawai a matsayin taron fadakarwa sai dai kawai ayi batun daukar kwakkwaran mataki kawai.
Ya ce ta hanyar ilmantar da al’ummar kasa game da Illolin miyagun kwayoyi da ke haifar da dimbin matsaloli musamman ta fuskar tashe tashen hankula, dom haka ne muke da kudirin samar da hanyoyin magance hakan domin jama’a cikin al’umma su samu dama goben su ta yi kyau.
Da yake jawabi a game da wadansu hukumomin kula da lafiyar jama’a na duniya kamar irinsu majalisar dinkim duniya da hukumar kula da lafiya ta duniya WHO duk abin da ya dace mu yi shi ne daukar matakan kariya na gaggawa, samar da gyara a harkokin dokokin mu da kuma gyara da jama’ar da illar ta sama.
“Domin samun nasarar wadannan abubuwan shi ya sa muke yin aikin hadin gwiwa da hukumar fadakarwa da wayar da kan jama’a ta kasa (NOA), da hukumar da ke yaki da hana sja da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da wadansu kuma muhimman masu ruwa da tsaki, haduwa tare da shugabannin al’umma, shugabannin gargajiya, shugabannin addinai,masu ilmantar da jama’a da kungiyoyin da ba na gwamnati ba a dukkan jihohin da kananan hukumomi a yankin arewa maso Yamma.
Saboda haka ya zama wajibi ga gwamnati da ta tashi tsaye domin samar da matalan da za su magance ainihin tushen wannan matsalar, sannan kuma shugabannin al’umma ya dace su rika nuna al’adun da ke nina kyama da shan miyagun kwayoyi da illolin da hakan ke haifarwa ga jama’a.
“Matakan da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke dauka domim magance wannan matsalar na nufin cewa matakai ne na samar da ingantattun sahihan gyare gyare don haka sai jama’a suma su dauki matakan da muhimmanci ta yadfa za su amfani kowane Dan Najeriya”.
“A saboda hakan ne muke yin kira ga daukacin shugabannin kananan  hikumomi da su shiga cikin wannan taarin yaki da wannan matsalar misamman ta hanuar yin aiki da hukumomin da ke wannan aikin ta yadda za a samu kwalliya ta biya kudin sabulu”.
Daga cikin kokarin da ake yi akwai samar da wani tsari da ake kira WADA wato yaki da matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi da ake yin fadakarwar har a makarantu da cikin al’ummat kasa a wurare daban
Bugu da kari kuma wadannan tagwayen kalubalen da ake fama da su Dole ne in yi godiya da jiniina game da irin kokarin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yadda yake bayar da abin da ake bukata domin maganin matsalar.
Haka kuma gwamnatin tarayya ta kara karfafa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta hanyar bayar da makudan kudi, samar da kayan aiki na zamani da kuma bayar da horo da kuma samar da ayyikan gyare gyaren hankali da dabi’un masu ta’ammali da miyagin kwayoyi da kuma yin aikin haduwa da jama’a ko al’umma na can kasa domin wayar masu da kai game da illar miyagin kwayoyi.
Wannan matakan da gwamnati ta daika ya haufarwa da masu safarar miyagin kwayoyi mataala ya kuma sabawa wadansu jama’a sauki da suka kasance suna ta’ammali da kwayoyi miyagu.
A cikin shekaru hudu mun yi aikin fadakarwa a makarantu a kalla har sau dubu 9,239 hakan ya hada da wuraren Ibada, wuraren aiki, Tashoshin mota da cikin jama’a da dai sauransu da aka samu a kalla mutane 3,333,678 da suka samu halarta.
Tun da farko da yake ganatar da jawabi a wajen taron shugaban hukumar fadakarwa da wayar da kan jama’a ta kasa (NOA) Lanre Isa Onilu cewa ya yi wannan taron ana korarin samar da kariya ne ga matasan mu game da illar yaduwar miyahin kwayoyi a cikin al’ummar mu.
Ya ce a cikin Najeriya hakika wannan matsalar ta shan miyagun kwayoyi ta lalakta rayuwar jama’a da dama, amma a yanzu fa mina cewa ya isa haka nan domin za mu fara yin fadakarwa game da illar a makaranti da cikon jama’ar mu a ko ina suke a yankin arewa maso Yamma.
Ya ci gaba da bauanin cewa wasu matasa da ke da kananan shekaru da dama sun shiga cikin wannan matsalar ta shan miyagun kwayoyi ta hanyar wadansu da suke rayuwa tare da su sai suka jefa su cikin matsalar haka kuma masu yin ayyukan ta’addanci na yin amfani da miyagin kwayoyi domin kaaar da hankulan wadanda ake jefa wa cikin aokata miyagin ayyukan tayar da fitina.
Wannan gangami ne na yin aiki kai tsaye domin shugabannin al’umma, shugabannin ta yadda duk za su fadaka su kuma dauki sako zuwa ga inda ya dace musamman ga matasa da su fahimci illar da ke cikin lamarin don haka a yanzi ne ya dace a daiki
Dole ne sai min yi aiki a game da samar da kwararan tsare tsare domin ta yadda za a yi aiki da al’umma da suka hada da maya yan kasuwa da suke cewa su ne a kan gaba wajen yin yaki da wannan matsalar don haka a kawar da ita shi ne alkairi kawai.
Shugabannin gargajiya da Malamai a cikon al’umma na da raaar da za su taka ta fuskar fadakarwa da aikewa da sakonni ga jama’a a yankin arewa maso Yamma domin a cimma warware matsalar shaye shaye da duk wani nauyin yin ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Masu ta’ammali da miyagun kwayoyi na samun matsaloli kamar na rashin adalci a tsakanin jama’a, illar lalacewar mutanen gida ko iyali da suka hada da yaya,yan uwa da abokan arziki.
Sai ya yi kira ga daukacin iyaye da su sayo kayan yin gwajin da ake gano mai yin ta’ammali da miyagin kwayoyi domin a wasu lokutan sai dai ka ga mutum kawai amma ba a san abin da yara ke ciki ba sai lamarin ya baci kafin daga bisani a gane kuma kafin ma ya fantsama cikin gida har ya kawo matsalar rashin jituwa a tsakanin jama’a ko iyalin da ke gidan.
Ofishin kakakin majaliaar wakilai Dokta Abbas Tajuddeen da kuma hukumar fadakarwa da wayar da kan jama’a ta kasa NOA ne suka shirya wannan taron gangamin na shiyyar arewa maso Yamma da aka yi a Otal din 17 cikin garin Kaduna

About andiya

Check Also

Dokta Baffa Babba Dan Agundi Ya Tallafa Mutane Dubu Sha Biyar (15000)

….Datakta Janar na hukumar kula da ingantuwar ayyuka, Dokta Baffa Babba DanAgindi, ya bayyana cewa …

Leave a Reply

Your email address will not be published.