Domin samun ingancin gudanar da mulki a Masarautan Zazzau, Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR ya amince da canje – canje da kuma nada sababbin guraben Hakimai a Masarautar Zazzau kaman haka.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da ke dauke da sa hannun ABDULLAHI ALIYU KWARBAI,
Mai Magana Da Yawun Masarautar Zazzau da aka rabawa manema labarai.
1. Jakadan Nijeriya a Kasar Austria, TAFIDAN DAWAKIN ZAZZAU Ambasada SULEIMAN DAUDA UMAR a yanzun an daga darajan sa ya zuwa MAGAJIN DOKO sai,
2. MAJE KIRAN ZAZZAU, Alhaji IBRAHIM SANI ZUBAIRU yanzu an daga darajarsa zuwa WAMBAN DOKO sai,
3. Alhaji ABDULKARIM ZAILANI Sabon Hakimin Gunduman SABON BIRNI ya an bashi mukamin MAJE KIRAN ZAZZAU sai,
4. Sarkin Damau Alhaji AUWALU ALIYU DAMAU wanda aka daga darajanshi daga Sarki zuwa Hakimin Gunduman Damau zai ci gaba da rike matsayin Sarkin Damau Hakimin Gunduman Damau sai,
5. Injiniya IBRAHIM ABUBAKAR yanzun aka tabbatar masa da mukamin TAFIDAN DAWAKIN ZAZZAU sai,
6. Alhaji BASHIR NUHU SHITTU wanda shima aka tabbatar masa da sarautan SARKIN TUTAN ZAZZAU.