Home / Labarai / Ba Ruwan Mu Da Batun Yarjejeniyar Samowa – Dan Majalisa Abubakar Yalleman

Ba Ruwan Mu Da Batun Yarjejeniyar Samowa – Dan Majalisa Abubakar Yalleman

Daga Bashir Bello Majalisar Abuja

Dan majalisar Wakilai na tarayya mai wakiltar al’ummar kananan hukumomin Malamadori da Kaugama a cikin Jihar Jigawa Abubalar Makki Yalleman, ya bayyana ra’ayinsa a game da tattaunawar da majalisar ta yi kan batun yarjejeniyar Samowa da ake ta cece – cuce a kanta da ya bayyana cewa yan majalisar arewacin Najeriya sun fi kowa kalubalantar wannan batu na yarjejeniyar Samowa.

Dan majalisa Abubakar Makki Yelleman ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a majalisar jim kadan bayan kammala yin mahawara a kan lamarin.

Yalleman ya kara da cewa su a matsayinsu na yan majalisa kawai suna jin wai wai ne kawai a game da lamarin domin a dokar kasa kuma cikin kundin tsarin mulkin kasa doka ta ba majalisa dama cewa kowa ne irin Sakon hannu ko doka bangaren masu mulki za su yi dole ne sai an kaiwa majalisa ta sahale wa Gwamnati, amma a wannan batu na yarjejeniyar Samowa ba su ma hi an sa hannu ba Sam balantana majalisa ta sahale wa Gwamnati wato a amince ko a ki amincewa da ita. Amma dai ku a matsayinku na manema labarai kuna cikin majalisar nan kun kuma ga irin yadda aka yi ta tafka mahawara wannan ya fadi wancan ya fada kuma a karshe aka nuna rashin amincewar majalisa domin ba mu lamunta ba, saboda addinin mu da al’adun mu ba su zo mana da wannan tsarin ba ko kadan.

“Kuma shi a wannan al’amari duk inda ba rami me ya kawo zancen rami, balantana ace an sa hannu ba Kaza ba Kaza koma an cire kaza to, me ya kai ma har a cire Kaza da Kaza mu a matsayin mu na wakilan jama’a ba fa mun zo ne domin wakiltar kawunan mu ba al’umma muke wakilta. Saboda haka duk abin da adfininmu,al’adarmu,yankin mu duk suka nuna ba su bukata ba ruwan mu da shi domin mu wakilai ne kawai.

Da akwai” wadansu shugabannin mu a majalisar wakilai kamar irin Honarabul Ali Madaki da ke Wakiltar karamar hukumar Dala a Jihar Kano da dan majalisa Muktar mai wakiltar kananan hukumomin Yan kwashi, Roni da Kazaure daga Jihar Jigawa duk sun kawo kudirin rashin amincewa da wannan lamarin yarjejeniyar Samowa. Lallai a binciki wannan maganar ko ma a kwaita domin mu yan majalisa wai wai kawai muke ji ba a kawo shi gaban majalisa ba don haka dukkan mu da muka tashi a kan doron majalisa ana tattauna batun duk mun tabbatarwa da majalisar cewa ba ma cikin wannan ra’ayi ko ma idan akwai batun, sai dai inda ba rami me ya kawo zancen rami?

” Ace an cire kaza ko sakin layi kaza mu ba ma ciki wannan batu sam, kuma ai idan aka duba sosai ai akwai hanyoyin samun kudi ba wai sai an bi ta hanyar wannan Samowar ba”.

A game da batun kudirin dokar da dan majalisa Abubakar Makki Yalleman ya kawo gaban majalisar kuwa sai ya ce ya kawo kudirin dokar ne domin idan an yi ta za a samu inganta harkokin kiwon lafiya har ma a samu yi wa mazabarsa ta karamar hukumar Malamadori asibitin Gwamnatin tarayya, wanda kuma kudirin ya wuce karatu na farko sakamakon hakan ina cikin garin ciki da annashuwa  kwarai domin ya samu wuce wa karatu na biyu za a tura shi wajen kwamitin da ya cancanta su kira al’umma su nuna cewa wannan al’amari ya dace a kawai da dokar don a gina asibiti a cikin karamar hukumar Malamadori a Jihar Jigawa hakan kuma zai taimakawa a kalla mazabu biyar su ci ribar wannan aikin asibiti idan an yi shi, kai dai its Malamadori ta na tsakiya ne kawai don haka ta cancanta a yi asibitin a nan. Ta yi makwabtaka da mazabar tarayya ta Kuri, Kirikasamma ta kuma yi makwabtaka da Hadeja, Auyo da Kafin Hausa sannan kuma ta yi makwabtaka da Mai Gatari, Gumel, Sule Tankarkar da Gagarawa ta kuma yi makwabtaka da Ringim,Miga da Jahun don haka idan an lura muna da kananan hukumomi 27 sannan Jihar Jigawa na da yawan al’umma sama da Miliyan biyar amma irin wannan asibitin guda daya ne tal muke da shi don haka dukkan wadannan yankunan da na karanta a yanzu ya yi nisa da su baki daya saboda haka ne muke ganin lallai ya cancanta ayi wannan asibitin a inda nake yin bayani a kansa domin dukkan yankunan nan guda biyar da na lissafa suna zuwa ne makwabta neman magani a garin Unguru jihad Yobe kuma ga shi yanayin cututtuka sai lamarin ya fara shafar mu don haka idan an kawo wannan asibitin zai saukake abubuwa da dama har muma mu shiga cikin lalitar Gwamnatin tarayya mu kuma ji dadi ta fuskar yanayin kiwon lafiyar jama’a”.

A game batun hanyoyin da za su hada wannan yankin da dan majalisa Abubakar Yalleman ke magana kuwa, Sai dan majalisar ya ce idan mutum zai fita tun daga garin Kano zuwa Hadeja akwai sabon titin da aka yi don haka sai godiya domin wannan hanya sai mutum ya wuce mazabun Sule Tankarkar, Gumel, Kaugama, Malamadori har a Isa Hadeja , don haka muna yi wa Allah godiya kasancewar shugabannin mu da suka shude da wadanda ke ci a halin yanzu duk sun yi aiki kwarai na hada dukkan wuraren nan da hanyoyi da duk inda ka taso zaka iya zuwa ko’ina kake bukatar zuwa domin akwai hanyoyin da aka yi da suka hada ko’ina da ko’ina a fadin Jihar.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.