….Mu Bamu da wata matsala da kowa, inji Bafarawa
Imrana Abdullahi
A wajen wani babban taron zallan matasa masu jini a Jika tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa garkuwan Sakkwato tare da wadansu fitattun mutane yan arewacin Najeriya suka kaddamar da wata kungiyar matasa mai karfi domin ceton yankin Arewa da kasa baki daya.
A wajen taron yan jarida Bafarawa tare da Hajiya Naja’atu Muhamamd sun yi jawabai masu yawa bayan amsa tambayoyin manema labarai da suka halarci wurin.
Tsohon Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya bayyana cewa manufar kafa kungiyar neman ci gaban Arewa a kowane bangare ta (Northern star Youth emporwerment initiative) shi ne domin tabbatar da ganin an hada kan arewacin Najeriya da kasa baki daya da nufin samar da ingantaccen ci gaba a ko ina.
Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya bayyana hakan ne a wajen kafa wata sabuwar kungiyar da aka kafa domin ci gaban arewacin kasar da aka yi a dakin taro na gidan tunawa da Sardauna Ahmadu Bello da ke Kaduna.
Bafarawa ya bayyanawa matasa cewa za a bude ofisoshin wannan kungiyar a ko’ina a dukkan Jihohin arewacin kasar.
“Ina son in gaya wa matasan Najeriya cews sai sun ta shi tsaye domin su ne sabon jini da ake kira Digital kuma a yanzu mu tsofaffi ake kira analog don haka kowa na bukatar kowa domin idan an dauke wuta sai ayi amfani da analog idan kuma da wutar lantarki sai ayi amfani da Digital saboda haka sai an yi amfani tare da yin aiki tare.
Dalhatu Bafarawa ya ci gaba da bayani a wajen wani taron manema labarai bayan kaddamar da kungiyar matasan cewa suna maraba da duk wata kungiyar da za su yi wannan aikin ceton Arewa da kasa baki daya.
Sai Bafarawa ya fayyacewa taron yan jaridar cewa ba su da wata matsala da kowa don haka duk mai son bayar da gudunmawarsa tsoho ko matashi domin ceton Arewa da kasa baki daya ya hanzarta shigowa ana maraba da shi.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai kungiyoyin Musulmi da na Kirista da kuma Sakataren PDP na kasa Sanata Tsauri da tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna da sauran dimbin kungiyoyin da ke fafutukar kare yancin Arewa